Dan Majalisa Ya Yi Wa Yan Mata Marayu 9 Auren Gata a Jihar Zamfara, Hotuna Sun Bayyana

Dan Majalisa Ya Yi Wa Yan Mata Marayu 9 Auren Gata a Jihar Zamfara, Hotuna Sun Bayyana

  • Kabiru Maipalace, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ya yi wa wasu yan mata marayu tara auren gata a jihar Zamfara
  • Maipalace ya dauki nauyin yi wa yan matan kayan daki irin wanda ake yi wa kowace yar gata idan za ta yi aure
  • Dan majalisar ya yi nasiha ga amaren yayin da ya yi kira gare su da su bi mazajensu sau da kafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Gusau/Tsafe a majalisar wakilai ta kasa, Kabiru Ahmadu Maipalace, ya dauki nauyin auren wasu yan mata marayu tara, karkashin shirinsa na kula da jin dadin mata, marayu da marasa gata.

Da yake gabatar da kayan daki da sauransu ga amaren a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, Maipalace ya ce ya yi hakan ne don cika alkawarin zabe da ya daukarwa al'umma.

Kara karanta wannan

Yadda matashi dan shekaru 20 ya kashe mahaifinsa a Kaduna

An yi auren yan mata tara a Zamfara
Dan Majalisa Ya Yi Wa Yan Mata Marayu 9 Auren Gata a Jihar Zamfara, Hotuna Sun Bayyana Hoto: @KabiruAmadu_MP
Asali: Twitter

Maipalace wanda ya samu wakilcin sakatarensa, Mustafa Hassan a wajen taron, ya bayyana cewa wannan abu da ya yi yana daga cikin shirinsa na tallafawa marasa gata karkashin kwamitinsa kan mata, marayu da marasa gata, rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan ya ce:

"Karkashin kwamitin, mun gano mata marayu da marasa gata 41 da dan majalisar zai dauki nauyin aurensu kuma za mu fara da mutum tara a yanzu.
"A yau, mun gabatar da kayan daki seti tara da sauran kayan aure da dan majalisar ya yi wa wadanda suka amfana."

Dan majalisar ya bukaci amaren da su mutunta aurensu sannan su yi amfani da karamcin da aka nuna masu saboda gobensu.

Hukumar Hisbah ta yi martani

Haka kuma, shugaban hukumar Hisbah a jihar Zamfara, Umar Hassan, ya yaba ma dan majalisar sannan ya bayyana wannan taimako da ya yi a matsayin taimakon al'umma baki daya.

Kara karanta wannan

Dan caca da ya ciyo N102m zai taimakawa dalibin da yayi asarar kudin karatunsa a caca

Umar Hassan ya ce:

"Wannan zai taimaka wajen rade matsin tattalin arziki da laifuffuka cikin al'umma."

Ya roki masu hannu da shuni da su yi koyi da dan majalisar wajen taimakawa marasa gata.

"Ku bi mazajenku sau da kafa", an yi wa amaren nasiha

A martaninsu mabanbanta, sakatariyar kwamitin, Sadiya Mahe, da shugabar matan PDP a jihar, Kulu Master, sun yaba ma dan majalisar kan kulawar da yake ba mata.

Sun yi kira ga amaren da su yi amfani da damar aurensu da kyau sannan su mutunta mazajensu saboda amfaninsu nan gaba.

Ga hotunan amaren da kayan dakin da aka yi masu a kasa:

Za a sake auren gata a Kano

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta fara tantance wasu karin mutane 147 da za a daura wa aure a jihar.

Hukumar kare yaduwar cutar sida ita ta fara tantancewar don sanin matakin lafiyarsu kafin daura mu su aure, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng