"Adalci Muke So": NLC, TUC Sun Bai Wa FG Sharruda 6 Kafin Janye Yajin Aiki Na Gama-Gari

"Adalci Muke So": NLC, TUC Sun Bai Wa FG Sharruda 6 Kafin Janye Yajin Aiki Na Gama-Gari

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta fitar da wasu sharudda da gwamnatin Najeriya za ta cika kafin ta kawo karshen yajin aikin da ta shiga
  • NLC, ta lissafa sunayen wasu jami'an gwamnati, 'yan sanda, ciki har da tsohon kwamishan 'yan sanda na jihar Imo da take so a hukunta
  • A ranar Talata ne kungiyar kwadagon ta tsunduma yajin aikin gama gari, wanda ya jawo tsayawar komai a fadin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shuwagabannin kungiyar kwadago ta kasa NLC, sun bayyana wasu sharudda shida da ya zama wajibi a cika su kafin kungiyoyin kwadago a kasar su janye yajin aikin da suke yi.

Sun jera sharuddan shida a cikin wata sanarwa da suka fitar a shafin kungiyar na X (wanda aka fi sani da Twitter) ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye yakin aiki, sun bada dalili

Joe Ajaero
NLC ta kafawa gwamnatin tarayya sharudda shida kafin janye yajin aikin da ta shiga Hoto: Joe Ajaero
Asali: Twitter

Sharudda 6 da NLC ta kafawa gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta NLC ta ce, da farko dole ne a kama Chinasa Nwaneri, mai ba Gwamnan Imo shawara, da ake zargin shi ne ya jagoranci harin da aka kaiwa shugaban NLC da sauran ma’aikata a jihar, tare da kai shi gaban kotu.

Kungiyar ta kuma ce a kama dukkan jami’an ‘yan sanda da kuma ‘yan daba da ke da hannu a harin da aka kai wa shugaban kungiyar, a gurfanar da su gaban kuliya tare da korarsu daga aiki.

Haka kuma, ta bukaci a kama, gurfanarwa tare da korar babban jami’in tsaro a gidan gwamnatin jihar Imo, wanda aka fi sani da SP Shaba.

“Ya jagoranta tare da bayar da mafaka ga ‘yan daba don muzgunawa ma’aikata a jihar Imo,” NLC ta yi zargin.

Kara karanta wannan

Cin zarafin Ajaero: Majalisar tarayya za ta saka baki kan yajin aikin kungiyar kwadago

Sauran sharuddan NLC

Wani sharadi da kungiyar kwadago ta bayar shi ne kamawa, hukuntawa da kuma korar wani kwamandan ‘yan sandan da ba a bayyana sunansa ba, wanda ta ce shi ne ya ba da damar cin zarafin shugaban NLC da sauran ma’aikata a jihar.

Sharadi na shida don kawo zaman lafiya shi ne cewa, dole ne a binciki tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Ahmed Barde, tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zarginsa da hannu wajen cin zarafin shugaban NLC.

“Bukatunmu masu sauki ne. Muna neman adalci".

- Cewar NLC

NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki

Kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito, kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.