Jami'an tsaro sunyi nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar asiri na Don Waney

Jami'an tsaro sunyi nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar asiri na Don Waney

- Jami'an tsaro sunyi nasarar kashe daya daga cikin kwamandojin kungiyar asiri na marigayi Don Waney wanda suka kashe mutane 23 a jihar Ribas kwanakin baya

- Austin Agulegbu ya kasance shine babban jami'in tsaro ga marigayi Don Waney kuma kwamanda na shida a kungiyar asirin

- Bayan an gano inda yake buya a karamar hukumar Obiaruku da ke jihar Delta, Jami'an tsaro sun kai masa samame inda ya mutu wajen artabu da su

A cigaba da biyaya ga umurnin shugaba Muhammadu Buhari na binciko wadanda suke da hannu kan kisan mutane 23 a garin Omuku da ke karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni na 'yan kungiyar gawurtacen jagoran kungiyar asiri, marigayi Don Waney, Sojin Najeriya tare da hadin gwiwa da jami'an Dss sunyi nasarar kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar mai suna Austin.

Jami'an tsaro sunyi nasarar kawar da wani kwamanda daga kungiyar Don Waney
Jami'an tsaro sunyi nasarar kawar da wani kwamanda daga kungiyar Don Waney

Austin Agulegbu ya kasance shine ne shida a mukami a kungiyarasirin kuma babban jami'in tsaro ga marigayi Don Waney.

KU KARANTA: Hukumar Sojin Najeriya ta shawarci Shekau ya mika wuya

Bayan lokaci mai tsawo da jami'an tsaron suka dauka suna gudanar da bincike dare da rana, sun gano inda ya ke buya a layin sabuwar sapele da ke karamar hukumar Obiaruku na jihar Delta inda suka kai masa samame a sadiyar 14 ga watan Febrairun 2018.

Agulegbu ya mutu sakamakon musayar wuta da ya yi da jami'an tsaron kuma a halin yanzu a tafi da gawar sa zuwa jihar Ribas inda aka mika ga rundunar yan sanda.

Ingantaccen bayyanai da Jami'an tsaron suka samu ya nuna cewa akwai sauran yan kungiyar da ke yawo cikin jihar kuma suna shirin sake kai hari cikin yan kwanakin nan, hakan ya sa jami'an tsaron ke tsananta bincike domin kama su kafin su kai ga kai harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164