Ana Neman N35m Don Dawo da Gawar Dalibin Najeriya da Aka Kashe a Philippines, Cewar Gwamnati

Ana Neman N35m Don Dawo da Gawar Dalibin Najeriya da Aka Kashe a Philippines, Cewar Gwamnati

  • Akalla ana neman naira miliyan talatin da biyar don dawo da gawar wani dalibin Najeriya da aka kashe a kasar Philippines
  • Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin wasu 'yan kasar China da laifin kashe Emmanuel a ranar 23 ga Oktoba, 2023
  • Kazalika, za a iya kashe naira miliyan 10 zuwa naira miliyan 15 don kona gawarsa a cikin kasar Philippines

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasar Philippines - Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta ce za ta kashe naira miliyan 35 domin dawo da gawar wani dalibin Najeriya mai karantun likita, Chibuikem Emmanuel, da aka kashe a kasar Philippines.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin wasu 'yan kasar China da laifin kashe Emmanuel a ranar 23 ga Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

Chibuikem Emmanuel
Ana zargin gungun 'yan China ne suka yi wa dalibin Najeriyar kisan gilla Hoto: Michael Ojuola
Asali: Twitter

Michael Ojuola ya wallafa hakan shafinsa na dandalin sada zumunta na X, wanda ya bayyana Emmanuel a matsayin abokinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe Emmanuel - Ojuola

Ojuola ya wallafa cewa, gungun 'yan China sun yi wa dalibin Najeriyar kisan gilla.

Ya rubuta:

"Sun ɗaure hannunsa sama, suka rufe fuskarsa sannan kuma suka ɗaure bakinsa, suka yi masa dukan kawo wuka har sai da rai yayi halinsa,"

A ranar Talata, darakta a ma'aikatar harkokin waje, Ambasada Enya Francis, ya ce ma'aikatar tana da kusanci da ofishin jakadanci na Philippines, kuma tana kan gudanar da bincike.

Kudaden da gawar Emmanuel za ta lakume

Haka zalika, shugaban hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Francis, ya yi karin haske kan lamarin a wani zaman bincike da majalisar dattawan hukumar ta gudanar.

“Har yanzu ba a yi jana’izar gawar Ikem ba, saboda za a kashe akalla naira miliyan 31 zuwa naira miliyan N35 don dawo da gawar zuwa Najeriya."

Kara karanta wannan

Yajin aikin gama gari: Ma’aikatan Taraba sun bijire wa umurnin NLC, kowa ya tafi wajen aiki

"Sannan za a kashe akalla naira miliyan 10 zuwa naira miliyan 15 idan aka ce a kona gawar a Philippines,”

- Cewar Francis.

Ya kara da cewa, kudin ajiye gawar a gidan jana’izar yana kamawa naira 30,000 a kullum, don haka akwai bukatar a gaggauta daukar mataki kan binciken.

Yayar Emmanuel, Blessing Essien, ta bayyana cewa shi kadai ne namiji a gidan, kuma bisa ga al'adar Igbo, zai zama abin alfahari a dawo da gawar Najeriya don binne shi.

Najeriya na neman hakkin Ibrahim Bello da aka kashe a Cyprus

Legit Hausa ta ruwaito maku yadda hukumar ‘yan Najeriya a kasashen waje, ta bukaci a kwato hakki biyo bayan mutuwar wani dalibi dan Najeriya a arewacin Cyprus, Mista Ibrahim Khaleel Bello.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.