Najeriya na neman hakkin danta, Ibrahim Khaleel Bello wanda aka kashe a kasar Cyprus

Najeriya na neman hakkin danta, Ibrahim Khaleel Bello wanda aka kashe a kasar Cyprus

Shugabar hukumar ‘yan Najeriya a kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bukaci a kwato hakki biyo bayan mutuwar wani dalibi dan Najeriya mai shekaru 25 a arewacin Cyprus, Mista Ibrahim Khaleel Bello, da sauran al’ummanta da aka kashe a kasar.

Hukumar ta bayyana a wasu jerin wallafa da ta yi a twitter cewa “Ibrahim Khaleel Bello na daga cikin kimanin ‘yan Najeriya 100 da aka kashe cike da ban al’ajabi daga 2016 zuwa 2020 ba tare da hukunta ko daya daga cikin makasan ba.”

Misis Dabiri ta yi wannan roko na kwato hakkin ne biyo bayan wani korafi daga Justis Amina Ahmad Bello, wata kuliya a babbar kotun jihar Kaduna kan mutuwar ban mamaki na danta.

Ya kasance a shekararsa ta uku inda yake neman digiri a fannin injiniya a jami’ar Girne American a Girne (Kyrenia), Jumhuriyar Turkiyya na arewacin Cyprus( TRNC).

Dabiri-Erewa ta yi kira ga iyaye da su daina tura yaransu arewacin Cyprus domin Majalisar Dinkin Duniya bata san da ita ba illa Jumhuriyyar Turkiyya, inda ta kara da cewar Najeriya bata da alakar daflomasiyya da wannan kasa.

Najeriya na neman hakkin danta, Ibrahim Khaleel Bello wanda aka kashe a kasar Cyprus
Najeriya na neman hakkin danta, Ibrahim Khaleel Bello wanda aka kashe a kasar Cyprus Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Ta ce lallai ya kamata a sanya wannan kasa a bakin littafi sakamakon yawan daliban Najeriya da suka yi mutuwar ban al’ajabi a kasar ba tare da gurfanar da wani ko biyan diyya ba.

Ta ba tawagar karkashin jagorancin Bello tabbaci cewa hukumar NIDCOM za ta yi aiki da ma’aikatar shari’a, hukumar Najeriya a Turkiyya da sauran hukumomin da ya kamata domin tabbatar da an yi adalci.

Ta kara da cewar : mutuwar Ibrahim Khaleel Bello ya zama izina na kawo karshen ci gaba da kashe-kashen daliban Najeriya a wannan kasa.

Dabiri ta bayyana cewa mafi akasarin fanonnin da iyayen Najeriya ke tura ‘ya’yansu domin karantowa a jami’o’in arewacin Cyprus basu da lasisi kuma sai a kare da kashe masu yara, ba a kai rahoton yawacinsu ba.

Ta ce: “Lokaci ya yi da za mu sanya dukkanin jami’o’in arewain Cyprus a bakin littafi sannan mu shawarci dalibanmu daga neman gurbin karatu a chan domin hatsari ne ga rayuwarsu da makomarsu a nan gaba."

Ta kara da cewar ofishin Atoni Janar na tarayya ta rigada ta sanar da lamarin ga ‘yan sandan kasa da kasa domin ci gaba da bincike.

Justis Amina Ahmad Bello, mahaifiyar marigayin ta ce tana so a bi hakki ne ba wai don saboda danta ba illa saboda sauran daliban Najeriya wadanda aka kashe a kasar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi sabbin nade-nade shida, ya ambaci Kangiwa a matsayin shugaban PWDC

Ta yi bayanin yadda aka kashe mata 'da sannan hukumomi a arewacin Cyprus suka yi rufa-rufa da hukumomin jami’ar wadanda suka yi ikirarin cewa shi ya kashe kansa.

Sun yi ikirarin cewa ya fado ne daga bene mai hawa bakwai.

Ta ce lallai sai dai a yi bincike sannan a gurfanar da dukkanin wadanda ke da hannu a ciki domin babu abun da ke nuna danta ne ya kashe kansa.

Justis Bello ta ce ‘yan sa’o’i kafin a kashe mata da, ta yi magana da shi, sannan ya nuna tsoro game da rayuwarsa a jami’ar.

Ta ce: “Ban yarda cewar hatsari ko kisan kai bane domin n ace Cyprus sa’o’i 24 bayan faruwar lamarin sannan na je wajen ajiyar gawawwaki inda babu kurzunu ko ciwo a jikinsa. Kawai ina zargin cewa an kashe mani dana ne.”

Ta ce ‘yan sa’o’i kafin mutuwar yaron, ya aika mata sako ta WhasApp cewa : “Mama, dan Allah ina so na dawo gida. Wallahi idan na tsaya a nan, mutuwa zan yi ba tare da wani ya damu ba. Kawai ina son dawowa gida. Mama dan Allah ki fahimci cewa nan ba wajen zama na bane.”

Ta yi zargin cewa akwai yiwuwar an kwashe wasu muhimman kayan cikin mamacin domin an farke cikin dan nata kuma gawarsa na dauke da dinki a lokacin da aka sake shi.

Marigayi Ibrahim Khaleel Bello na cikin ‘yan Najeriya 100 da aka kashe a kasar daga 2016 zuwa 2020 ba tare da an hukunta wadanda suka aikata hakan ba, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel