An Kama Dalibin FUNAAB Kan Ciyar Da Budurwarsa Guba a Ogun

An Kama Dalibin FUNAAB Kan Ciyar Da Budurwarsa Guba a Ogun

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke wani dalibin ajin karshe a jihar Ogun, bisa zarginsa ya sanya wa budurwarsa tare da kawarta guba a jikin biredi
  • Saurayin, ya aikata hakan ne bayan da ya gayyaci budurwar tasa zuwa gidansa, yayin da ita kuma ta tafi da kawarta don ta raka ta
  • Sai dai an gaza gano dalilin saurayin na aikata wannan danyen aiki, amma rundunar 'yan sanda ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abeokuta, jihar Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani dalibin shekarar karshe a jami’ar aikin gona ta tarayya da ke Abeokuta, mai suna Oladokun Ayomide.

Kara karanta wannan

Yajin aikin gama gari: Ma’aikatan Taraba sun bijire wa umurnin NLC, kowa ya tafi wajen aiki

Rundunar ta kama Ayomide bisa zarginsa da kashe budurwarsa mai suna Ugbokwe Mmasichukwu da wata mata mai suna Odumosu Semilore.

Jami'ar noma ta Abeokuta
Dalilibin, ya sanya wa budurwar da kawarta gubar ne bayan da suka je gidansa a Abeokuta Hoto: FUNAAB
Asali: UGC

Me ya kai Ugbokwe Mmasichukwu gidan saurayin?

Rundunar ‘yan sandan ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da gubar da ake kyautata zaton hadawar barasa, da kuma wani sinadari mai cutarwa da ba a gano ko menene ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya aikata hakan ne bayan da ya gayyaci budurwar tasa zuwa gidansa da ke unguwar Surulere a unguwar Camp da ke Abeokuta, a ranar Juma’a.

PUNCH Metro ta tattaro cewa a yayin da take barin gidanta zuwa gidan wanda ake zargin, Mmasichukwu ta fadawa abokiyar karatunta, Semilore, ta raka ta wurin saurayin nata.

Rundunar 'yan sanda ta fara bincike

Bayan shayar da su sinadarin da ake zargin guba ne, wakilinmu ya gano cewa, an garzaya da wadanda abin ya shafa asibiti, bayan da suka ci biredin mai guba.

Kara karanta wannan

Zaben 11 ga watan Nuwamba: Jerin gwamnonin jihar Bayelsa daga 1999 zuwa yanzu

Ko da yake kawo yanzu ba a san dalilin da ya sa wanda ake zargin ya aikata wannan danyen aiki baba.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta shaida wa wakilinmu cewa binciken farko ya nuna cewa, ana zargin Ayomide da niyyar cutar da wadanda abin ya shafa.

Mmasichukwu da Semilore na samun kulawar likitoci

Babban jami’in tsaro na kwalejin ilimi ta tarayya, Osiele Abeokuta, Olusola Ajibola, shi ya ya jagoranci cafke wanda ake zargin.

Ajibola ya shaidawa ‘yan sanda cewa, Mmasichukwu da Semilore daliban makarantar ne, yayin da Ayomide kuma dalibin makarantar FUNAAB ne a shekarar karshe.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sanda, Omolola Odutola, ya shaida wa wakilinmu cewa wadanda abin ya shafa na karbar magani.

Ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Dalibi ya kashe mahaifiyarsa a Anambra

Wani dalibi, Ekenedilichukwu Okeke, ya yi bayanin yadda ya halaka kishiyar mahaifiyarsa saboda rashin bashi Naira miliyan 1 kudin makaranta, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kama wani da kokon kan mutum sabon yanka a Ibadan, hotuna sun bayyana

Okeke na cikin wadanda ake zargi 20 da kwamishinan yan sandan jihar Anambra, CP Echeng Echeng ya yi hole a Awka, jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.