Shahararren Jarumin Fina-Finan Najeriya Mista Ibu Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana

Shahararren Jarumin Fina-Finan Najeriya Mista Ibu Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana

  • A watan Oktoban 2023, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya bayyana cewa yana fama da rashin lafiya da ke barazanar sanya wa a yanke ƙafarsa ɗaya
  • Fitaccen jarumin ya yi kira ga masoyansa da sauran jama'a da su taimaka masa da addu'o'i da kuma taimakon ƙudi domin ya biya ƙudin magani
  • Duk da cewa daga baya ya rasa ƙafarsa ɗaya, amma ana ta yaɗa jita-jita a shafukan sada zumunta cewa ya rasu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Enugu, Jihar Enugu - Wani rubutu da aka buga a Najeriya a shafin sada zumunta na Facebook, game da zargin mutuwar wani fitaccen ɗan Najeriya, ya fara yawo tun watan Oktoban 2023.

An yi zargin cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, John Ikechukwu Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya mutu.

Kara karanta wannan

Magidanci ya bindige abokinsa a Adamawa, ƴan sanda sun ɗauki mataki

Mista Ibu bai mutu ba
Shahararren jarumin Nollywood Mista.Obu yana nan a raye Hoto: Dr. Uche Nworah, Mr ibu
Asali: Facebook

Mista Ibu wanda haifaffen jihar Enugu ne yana fama da ƙalubalen rashin lafiya da ya janyo masa rasa ƙafarsa ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rubutun na ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba na cewa:

"Ɓarka dai kowa da kowa na zo nan don sanar da ku cewa JOHN OKAFOR wanda aka fi sani da Mista Ibu ya rasa ransa ƴan mintuna kaɗan da suka wuce."

An kuma sake bayyana wannan batun a Facebook nan da nan.

A yammacin ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, Legit.ng ta cigaba da ganin wannan iƙirarin a shafin wani mai amfani da shafin Facebook. Duba nan.

Masu amfani da Facebook da dama sun aika da saƙon ta'aziyya.

Amma Okafor ya mutu? Legit.ng ta yi bincike.

Tauraron Nollywood, Mista Ibu yana raye

Idan aka yi la’akari da yadda Mista Ibu ya shahara a Najeriya, da labarin mutuwarsa ya shiga kanun labarai da a ce gaskiya ne.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bai wa asibiti gudunmawar naira miliyan 20, ya bayyana dalili

Kafofin yada labarai sun ba da rahoton cewa Mista Ibu yana murmurewa daga tiyatocin da aka yi masa, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Legit.ng ta yanke hukuncin cewa Mista Ibu yana nan da ransa.

Saraki Ƴa Ɗauki Nauyin Jinyar Mista Ibu

A wani labarin kuma, gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ta biya dukkanin kuɗaɗen asibitin jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu.

Gidauniyar ta ce tana matuƙar farin cikin taimakawa Mista Ibu wanda ya daɗe yana fina-finan barkwanci fiye da shekaru 40 da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng