Yadda Tagwaye Suka Auri Tagwaye a Rana Daya, Hadaddun Hotunan Bikin Sun Bayyana
- Wasu tagwaye masu kama daya, masu suna Chukwuma da Chijioke, sun angwance a rana daya
- Abu mafi ban sha'awa a lamarin aurensu shine tagwayen mazan za su auri wasu tagwaye ne
- Hotunan shgalin bikinsu wanda aka yi a jihar Ebonyi ya bayyana a soshiyal midiya, kuma ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wasu tagwayen maza masu suna Chukwuma da Chijioke, sun auri rabin ransu, Chiwendu da Oluchi, a rana daya.
Ebonyi State Current News ta rahoto cewa tagwayen mazan sun auri tagwayen matan a jihar Ebonyi.
Legit Hausa ta tattaro daga katin gayyatan auren ma'auratan cewa an daura auren nasu ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Nuwamba a cocin St James Parish, Ihie, Amasiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hotuna daga shagalin bikin ya nuno yadda tagwayen amaren suka yi kyau cikin dogayen rigunansu na aure sannan mazajen na sanye da kwat da wando.
Wani hoto ya nuno ma'auratan suna yanka kek din aurensu a tare. Jama'a sun taya ma'auratan murna yayin da labarinsu ya karade soshiyal midiya.'
Jama'a sun yi martani
It'z Cynthia ta ce:
"Wow.
"Na taya su murna."
Afoke Jacinta ta ce:
"Wannan ya yi kyau na taya su murna."
Arinze Christian ya ce:
"Kai kai wannan abun farin ciki ne na taya su murna ❤️❤️❤️❤️❤️ har jihar Ebonyi."
Kenneth Ogbonnaya ya ce:
"Ina taya tagwayen mata murna, ku duka biyun za ku dauki juna biyu a rana daya da sunan Yesu Amin."
Emmanuel Odeke ya ce:
"Na taya ku murna, Allah ya rigada ya albarkaci sabbin gidajenku."
Engr Emmanuel Friday Nwanjatex ya yi martani:
"Na taya su murna."
Tagwaye sun haifi tagwaye
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani hoto da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno wasu jarirai hudu da wasu tagwayen mata biyu suka haifa.
Tagwayen matan ne suka haifi yaran hudu a matsayin yan bibbiyu yan awanni a tsakani, kuma sun yi aure ne a rana guda.
Wani abun da zai kara ba mutane sha'awa shine cewa iyayen yaran maza ma tagwaye ne kuma tare aka haife su.
Asali: Legit.ng