Magidanci Ya Bindige Abokinsa a Adamawa, Ƴan Sanda Sun Ɗauki Mataki
- Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta sanar da cafke wani magidanci bisa zarginsa da laifin harbe abokinsa
- Magidancin mai suna Wawe Nokomari wanda yake da ƴaƴa takwas ya aikata wannan aika-aikar ne bayan ya kwankwaɗi barasa
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan ya tabbatar da cewa rundunar na cigaba da bincike domin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa - Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wani magidanci mai suna Wawe Nokomari bisa zarginsa da harbin wani abokinsa, Ham Musa da bindiga.
Nakomari mai shekaru 45, wanda yake da ƴaƴa takwas, wanda ya fito daga ƙauyen Jabi a ƙaramar hukumar Shelleng a jihar Adamawa, an yi zargin ya buɗe wa abokin na sa wuta, inda ya samu munanan raunuka, cewar rahoton Leadership.
Jami'in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa wanda abin ya shafa na raye kuma a halin yanzu yana samun kulawa a asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa magidancin ya harbi abokinsa?
Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya sha barasa ne, sannan ya harbi abokinsa a lokacin da yake aiki a gonar shinkafa.
An dai yi zargin cewa mutanen biyu sun daɗe sun ƴar tsama da juna, wanda hakan ya sa Nokomari ya buɗe wa Musa wuta da bindigar da ya aro daga hannun wani ɗan banga, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Nguroje, wanda ya yi wa wanda aka harba tambayoyi, ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Afolabi Babatola ya umarci sashen binciken manyan laifuka ya binciki lamarin.
IGP Egbetokun ya yi magana kan dukan da aka yi wa shugaban ƙungiyar ƙwadago, ya aike da muhimmin saƙo
Nguroje ya ce kwamishinan ya bayar da umarnin cafke ɗan bangan da wanda ake zargin ya ari bindigarsa. Ya ce rundunar za ta tabbatar da gurfanar da wanda ake zargin bayan kammala bincike.
Matar da Ta Ƙona Mijinta Ta Shiga Hannun Ƴan Sanda
A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta sanar da cafke wata matar aure wacce ta watsawa mijinta tafasashshen man gyaɗa.
Matar mai suna Hope Nwala ana zargin ta da watsawa mijinta, Ekelediri Nwanko man gyada kan wata karamar jayayya.
Asali: Legit.ng