Babu Kudi: Takardun Nairori Sun Fara Gagarar Mutane a Gari Duk da Matakin CBN
- Tun daga Kano, Katsina, Jigawa, Adamawa har zuwa garuruwan Legas da Abuja, ana shan wahala wajen samun kudi
- Takardun Nairori sun yi matukar wahala a bankuna da kasuwanni, a karshe doke mutane su ka koma aika kudi ta banki
- Abubuwa sun tsaya cak a wuraren da ba a cinikin zamani domin ba a iya samun kudi a bankuna, na’urorin ATM ko POS
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Bincike ya nuna har yanzu ana faman wahala wajen samun takardun kudi, duk da za a cigaba da amfani da tsofaffin Nairori.
Mazauna garuruwan Legas, Abuja, Kano, Katsina, Jigawa, Adamawa da sauransu sun shaidawa Daily Trust cewa Nairori sun yi wuya.
Wannan matsala ta shafi kasuwanci da ake yi a kasuwanni musamman wadanda ke Arewacin Najeriya, an hakura da cinikin takardu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu kudi a POS da bankuna
Legit ta zagaya wasu na’urorin ATM da ke bankuna a garin Kaduna, ta fahimci ba a samun masu cire kudi kamar yadda aka saba a baya.
Wani mai sana’ar POS ya fada mana dole suka kara kudin da su ke karba idan an cire kudi saboda yadda takardun su ka yi masu wahala.
Wani ma’aikacin banki a Abuja ya shaida mana ana matukar fama da karancin Nairori musamman daga karshen makon da ya wuce.
"Ai abin ya kare rikicewa, daga shekaran jiya (a karshen makon can), sai dai a ba mutum N5000 kacal.
Ko ina mutum ya je N5000 kurum za a iya ba shi, sai dai ya yi hakuri domin babu kudi sosai a yanzu."
- Ma'aikacin banki a Abuja
Ya ake yi da Naira a kasuwa?
Kamar yadda wani ma’aikacin bankin da za mu iya bayyana sunansa ba ya fada mana, mutum ba zai iya samun fiye da N10, 000 kacal ba.
Rahoton ya ce wahalar kudin ya kawo cikas a kasuwannin da ke wasu kauyukan Kano, Katsina, Jigawa, Adamawa, Kaduna da kuma Taraba.
Masu kasuwanci a kauyukan kan iyaka su kan so a biya su da tsabar kudi wanda ya yi wahala, har masu POS suna kokawa da karancin Nairorin.
Har a Legas a kudancin kasar, samun kudi ya yi wahala a lokacin da ake cinikin karshe shekara, ‘yan canji kuwa sun koma aika kudi ta salula.
Menene ya jawo wahalar Naira?
Kwanakin baya aka samu rahoto cewa a wasu wurare yanzu sai mutum ya biya N150 a maimakon N100 zai samu N10, 000 a POS a jihohin Arewa.
Masu neman kudi masu yawa sai dai su yi hakuri ko su sha wahala kafin su samu.
Asali: Legit.ng