'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda a Katsina, Sun Ceto Mutum 3
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile yunƙurin kai wani harin ta'addanci da ƴan ta'adda suka yi a ƙaramar hukumar Jibia
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Katsina
- Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa jami'an ƴan sanda na Jibia sun ceto mutum uku da miyagun ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a ƙauyen Gogalo da ke ƙaramar hukumar Jibia ta jihar.
Rundunar ƴan sandan ta kuma samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su, cewar rahoton Daily Trust.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ASP Aliyu Abubakar-Sadiq ya fitar ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba a Katsina, rahoton The Guardian ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"A ranar 11 ga watan Nuwamba, da misalin ƙarfe 10:46 na dare, an samu bayanai a ofishin ƴan sanda reshen Jibia cewa ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai irin su AK-47, sun farmaki ƙauyen Gogalo tare da yin garkuwa da mutum uku."
"Da samun wannan rahoton, DPO na ƴan sandan Jibia, ya yi gaggawar tura tawagar bincike da ceto zuwa ƙauyen."
Tawagar ta cigaba da zagaye dazukan da ke yankin har zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 6:00 na safe, inda suka samu nasarar gano inda miyagun su ke tare da artabu da su."
"Dukkanin waɗanda aka yi garkuwa da su an yi nasarar ceto su ba tare da sun samu rauni ba. Ana cigaba da kokarin cafke wadanda ake zargin da suka gudu tsere yayin da ake cigaba da gudanar da bincike."
IGP Egbetokun ya yi magana kan dukan da aka yi wa shugaban ƙungiyar ƙwadago, ya aike da muhimmin saƙo
An Halaka Fitaccen Mai Garkuwa da Mutane a Katsina
A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar sheƙe wani fitaccen mai garkuwa da mutane a jihar.
Jami'an ƴan sandan sun halaka Nazifi Ibrahim, mai shekaara 22 a duniya a ƙauyen Unguwar Tsamiya da ke ƙaramar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng