Labari Mai Zafi: DSS da EFCC Sun Dura Rumfar da Dino Melaye Zai Dangwala Kuri’a
- Hukumar tsaro na DSS ta aika jami’ai na musamman zuwa Ayetoro-Gbede da ake shirin zaben sabon Gwamna a Kogi
- Dino Melaye wanda yake rike da tutar jam’iyyar adawa ta PDP ya na cikin wadanda su ke zabe a inda aka kai DSS
- Tun da safe ‘dan takaran na jam’iyyar PDP ya fara shelar cewa an samu takardun zabe dauke da sakamako na bogi
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kogi - Jami’an hukumar tsaro na fararen kaya watau DSS suna bakin aiki yayin da ake zaben gwamna a jihar Kogi.
A yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba 2023, Punch ta kawo rahoto cewa an ga jami’an tsaron a yankin Ayetoro-Gbede.
Dakarun sun je rumfar da ‘dan takaran PDP a zaben jihar watau Dino Melaye yake kada kuri’a a karamar hukumarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an DSS, EFCC v Dino Melaye
Zuwa yanzu ba mu da labarin abin da ya faru a wajen yayin da ake kokarin yin zabe.
The Cable ta ce har da jami'an EFCC masu yaki da rashin gaskiya aka gani a rumfar zaben domin maganin sayen kuri'a.
Bisa al’ada, jami’an tsaro suna sintiri domin tabbatar da cewa abubuwa suna tafiya lafiya kalau a lokacin da ake yin zabe.
Ina Dino Melaye ya shiga?
A cewar wani masoyin jam’iyyar APC da ke adawa da Dino Melaye, har yanzu ‘dan takaran bai fito rumfar zabe ba tukuna.
Rahotanni sun ce ma’aikatan hukumar INEC su na shirye-shirye domin ganin mutane sun fara zaben ‘dan takaran na su.
Dino Melaye ya na cikin wadanda su ka ci burin gaje kujerar Yahaya Bello wanda wa’adinsa yake shirin karewa a mulki.
Da Dumi-Dumi: "Gagarumin Magudi a Dukkan Rumfunan Zaben Kogi" Dino Melaye Ya Zargi APC Da Magudin Zabe
Dino Melaye yana zargin magudi
Kafin nan an ji Dino Melaye ya fito shafin Twitter yana ikirarin an kama malaman zabe dauke da wasu takardun bogi.
Tun kafin a fara dangwala kuri’a, Sanata Melaye ya ce an samu takardun da aka rubuta sakamako na karya suna yawo.
Hotuna sun nuna har an rubuta cewa APC ta samu kuri’u fiye da 500 a wani akwati da ke Eika a karamar hukumar Okehi.
Hukumar INEC na binciken magudi
INEC ta yi alkawarin cewa ma’aikatanta za su gudanar da bincike a game da zargin yayin da ake sauraron yadda za ta kaya.
Masana suna ganin zaben jihar tsakanin ‘yan takaran APC, PDP da kuma SDP ne.
Asali: Legit.ng