IGP Egbetokun Ya Yi Magana Kan Dukan da Aka Yi Shugaban Ƙungiyar NLC, Ya Aike da Muhimmin Saƙo
- IGP Kayode Egbetokun, ya yi tsokaci kan dukan da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a wata zanga-zanga a jihar Imo a makon jiya
- Shugaban ƴan sandan ya umarci mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ya gudanar da bincike kan lamarin
- Egbetokun ya ƙara da cewa babban maƙasudin binciken shine gano haƙiƙanin abubuwan da suka auku da ɗaukar mataki bayan binciken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kayode Adeolu Egbetokun, Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin dukan da aka yi wa shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) Kwamared Joe Ajaero.
A cewar gidan talabijin na TVC, shugaban ƴan sandan ya umarci mataimakin sufeto Janar mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ya binciki lamarin tare da gano haƙiƙanin abin da ya auku.
Egbetokun ya ce manufar farko ta tantance gaskiyar lamarin da kuma magance duk wata shubuha da za a iya samu ganin yadda aka ba ƴan sanda mabanbantan bayanai kan lamarin, wanda hakan ya sanya bincike ya zama wajibi domin gano haƙiƙanin abin da ya auku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me IGP ya ce kan dukan da aka yi wa Ajaero?
A cewar IGP a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 10 ga watan Nuwamba, rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi la’akari da muhimmancin yin riƙo da gaskiya da riƙon amanar jama’a.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a, musamman shugabannin ƙungiyar, cewa za a gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba, domin bayyana gaskiya.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyin kwadago da sauran jama’a da su kwantar da hankalansu, domin shi da kansa ya shiga tsakani domin magance matsalolin da suka dabaibaye wannan lamari.
A kalamansa:
"An fara bincike, kuma rundunar ƴan sandan Najeriya na bada tabbacin cewa za a gudanar da shi har zuwa ƙarshe, kuma za a ɗauki matakin da ya dace dangane da sakamakon binciken."
Ajaero Ya Magantu Kan Dukan da Ya Sha
A wani labarin kuma, Joe Ajaero shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ya yi magana yadda ya sha dukan tsiya a hannun jami'an tsaro a jihar Imo.
Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya bayyana cewa da rabon yana da sauran kwana ne a duniya, amma irin dukan da aka yi masa, ka iya sanya wa mutum ya rasa ransa.
Asali: Legit.ng