Jami'an Tsaro Sun Halaka Masu Garkuwa da Mutane Mutum 4 a Jihar Kebbi

Jami'an Tsaro Sun Halaka Masu Garkuwa da Mutane Mutum 4 a Jihar Kebbi

  • Jami'an tsaro na ƴan sakai sun samu nasarar halaka masu garkuwa da mutane mutum huɗu a ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi
  • Ƴan sakan sun samu nasarar halaka miyagun ne bayan sun cafke mai kai musu bayanai wanda ya raka su zuwa maɓoyarsu
  • A fafatawar da ƴan sakan suka yi da masu garkuwa da mutanen, sun samu nasarar halaka su ba tare da ɗaya daga cikin ƴan sakai ya samu rauni ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Ƴan sakai sun halaka wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi.

An ce waɗanda ake zargin sun shafe shekaru suna ta’addanci a yankin kafin a kama su tare da halaka su, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dakarun sojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 100, sun samu nasarori masu yawa

Yan sakai sun halaka masu garkuwa da mutane
Yan sakai sun sheƙe masu garkuwa da mutane a Kebbi Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Twitter

An bayyana cewa dai an halaka miyagun ne biyo bayan cafke mai kai musu bayani da aka yi, wanda ya kai ƴan sakai zuwa maɓoyarsu a cikin daji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka halaka masu garkuwa da mutanen

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma'a, 11 ga watan Nuwamba, darektan tsaro na ofishin majalisar zartarwa ta jihar Kebbi, AbdulRahman Usman ya bayyana cewa:

"Bayan samun bayanan sirri da suka kai ga cafke mai ba da bayani ga ƴan bindiga, ya amince ya kai ƴan sakai zuwa inda suke ɓoye a cikin dajin. An halaka su ne yayin musayar wutar da suka yi da ƴan sakai."

Ya ƙara da cewa ƴan sakan sun kwana a cikin dajin inda suka jira har zuwa safe kafin su fara gumurzu da fatattakar ƴan bindigan, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun buɗe wa motar ɗalibai wuta, sun tafka mummunar ɓarna

"Mun yi farin ciki da yadda ƴan sakan suka dawo gida lafiya ba tare da sun samu raunuka ba." A cewarsa.

Ya yaba da kokarin ƴan sakai na yankin, inda ya ce suna taimaka wa wajen ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi na yaƙi da matsalar taro da ke cigaba da aukuwa a jihar.

Ƴan Bindiga Sun halaka.Mutane a Sokoto

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka aƙalla mutum 11 a wani mummunan hari da suka kai a wasu ƙauyuka biyu na jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a kauyuka biyu da ke yankin Gandi a ƙaramar hukumar Rabbah, jihar Sakkwato, inda suka sace dabbobi sama da 300.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng