Rahoto: Ɗangote Zai Siyar Da Katafaren Jirgin Alfarma Da Ya Siya Don Murnar Ranar Haihuwarsa
- Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya shirya sayar da katafaren jirgin sama mai zaman kansa da ya biya miliyoyin daloli domin mallakarsa
- Dangote ya sayi katafaren jirgin domin amfanin kansa shekaru 13 da suka gabata domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, amma yanzu yana son sayar da shi
- Rahotanni sun nuna cewa Dangote yana duba hanyoyin da zai rage wasu tarin kadarorinsa na alfarma da ya mallaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Rahotanni sun bayyana cewa hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote ya sanya wani katafaren jirgin samansa kirar Bombardier Global Express XRS a kasuwa don sayar da shi.
Ya biya dala miliyan 45.5 don mallakar jirgin mai zaman kansa a shekarar 2009 (shekaru 13 da suka gabata), lokacin da yake bikin cika shekaru 53 da haihuwa.
Shafin Billionaire.Africa ya ruwaito cewa, shugaban kamfanin simintin Dangote, ya yanke shawarar rage wasu daga cikin kadarorin alfarma da ya mallaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma ruwaito Dangote na shirin sayar da jirgin ruwansa na alfarma da ya sanya miliyoyin daloli wajen mallakarsa.
Cikakken bayanai kan jirgin Dangote da zai siyar
Nan da karamin lokaci ake sa ran mutane da kamfanoni za su fara gabatar da bukatar sayen jirgin saman, kirar Bombardier Global Express XRS, da aka yi wa farin fenti na Matterhorn, da shuɗi mai duhu, da ratsin jan zanen 'Peking', wadanda ke kawata gangar jikin jirgin, fuka fuki, da wutsiya.
Yana iya ɗaukar fasinjoji 14 zuwa 15 ba tare da takura ba, wannan wani jirgi ne da ya fi dacewa da attajiran da su ka mallaki biliyoyin naira.
Bangaren hagu na gaba na jirgin na dauke da kujerar zama da wurin hutawa ga ma'aikata, wanda aka kebe shi kawai don ma'aikatan jirgin a lokacin doguwar tafiya.
Binciken da Legit.ng ta yi a shafin intanet na Avbuyer, ya nuna cewa, ana sayar da irin wannan jirgin Bombardier Global Express XRS akan dala miliyan 18.5 (N14.85 biliyan).
Dangote Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 525 A Cikin Sa'o'i 24
Kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta dauki wasu matakai da su ka kawo cikas ga kasuwancin attajiran kasar, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.
Kafin daukar wannan mataki, mafi yawan attajiran na cikin jerin masu kudi 500 a duniya, wanda Dangote ke jagorantarsu a Najeriya da kusan Dala biliyan 21, Legit ta tattaro.
Asali: Legit.ng