Aliko Dangote ne na 64 a masu kudin duniya a yanzu (jerin sunayen biloniyan)
Kamfanin Bloomberg Billionaire Index ta kasance kamfani dake dauko jerin sunayen mutane masu arzikin duniya. An samar da bayanai game da lissafin arzikin su ne a shafukansu dake dauke da bayanai masu amfani. Ana samun lissafin ne a karshen kasuwancin kowace rana a New York.
Dangote wanda shinemai kudin Afrika na tsawon shekaru takwas shine kadai dan Najeriyan da ya shiga jerin manyan biloniya 500 da Bloomberg ta saki a sunayen masu kudin duniya da take saki duk shekara.
KU KARANTA KUMA: An samu matsala: Manyan kwamishinoni a hukumar INEC zasu yi murabus
Bisa ga Bloomberg har yanzu Jeff Bezos, shugaban AMAZON ne mafi kudi a duniya da yawan kudin da suka kai $136B yayinda Bill Gates da Warren Buffett suka zamo na biyu da uku da yawan kudi $98.5Bda $83.1B kowannensu a jerin sunayen biloniyan.
Legit.ng ta tattaro cewa sunayen yan Afrika biyar ne kadai suka shiga jerin sunayen Bloomberg na manyan biloniya 500, inda Dangote ya zamo a samansu.
Sauran yan Afrikan guda hudu sune Nicky Oppenheimer na Afrika ta Kudu, wanda ke a jeri na 216 da arzikin $7.05 biliyan; Johann Rupert na Afrika ta Kudu inda yake a jeri na 225 da arzakin $6.92b, na biyar kuma na karse a jerin shine Naguib Sawiris daga kasar Masar, shine kuma na 331 da kudi $5.12b.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng