Tashin Hankali Yayin da Aka Kama Wani da Kokon Kan Mutum Sabon Yanka a Ibadan, Hotuna Sun Bayyana
- Rundunar yan sandan jihar Oyo ta gurfanar da wani da ake zargin matsafi ne, Hassan Kolawole a Ibadan
- An tattaro cewa bai dade ba da aka kashe mutumin da aka samu kansa a hannun Kolawole domin dai sabon yanka ne
- Yan Najeriya a soshiyal midiya sun shiga damuwa da samun labarin kisan gillar da aka yi wa mutumin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Rundunar yan sanda a jihar Oyo ta gurfanar da wani da ake zargin matsafi ne, Hassan Kolawole a ranar 10 ga watan Nuwamba.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, an kama Kolawole mai shekaru 45 dauke da sabon kokon kan mutum a Ibadan, babban birnin jihar.
An kama matsafi da kokon kan mutum a Ibadan
An gurfanar da wanda ake zargin a hedkwatar rundunar da ke Eleyele a karamar hukumar arewa maso yammacin Ibadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Blueprint ta rahoto, an kama Kolawole ne a karamar hukumar Ona Ara.
Bayan karin bayani daga rundunar yan sandar, masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu.
Legit Hausa ta tattaro wasu martani daga dandalin X a kasa:
@IamBlaccode ya ce:
"A hankali Ibadan ya fara zama mabuya da kogon matsafa. Ku tuna da batun Soka da wasu labarai masu alaka...Ya zama dole mutum ya dunga taka-tsan-tsan da ginin karkashin kasa da kangon gine-gine da ke dazuzzuka, a nan suke aiwatar da mugun nufinsu."
@The_khemist ya yi martani:
"Wayyo Allah na, wadannan kashe-kashe. Allah ka taimake mu."
@pacifik_cruise ya yi martani:
"Babu alamun nadama ko danasani a fuskarsa mai karfin nan."
Doris Michael ta rubuta:
"Wannan ya yi muni."
@Street_king_007 ya rubuta:
"Asirin Disamba ya yawaita kowa na so ya wataya."
An kama fasto da kokon kai
A wani labarin, mun ji cewa jami'an 'yan sanda a jihar Ogun sun cafke wani Fasto mai suna Oyenekan Oluwaseyi da wasu mutane 3 kan mallakar kokon kai na dan Adam.
Legit ta tattaro cewa an tasa keyar wadanda ake zargin a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba zuwa ofishin 'yan sanda a jihar.
Asali: Legit.ng