Al-Noor: Shahararren Dan Kasuwar Arewa Ya Ba da Gudunmawar Makeken Fili Ga Masallacin, Ya Yi Bayani

Al-Noor: Shahararren Dan Kasuwar Arewa Ya Ba da Gudunmawar Makeken Fili Ga Masallacin, Ya Yi Bayani

  • Masallacin Al-Noor da ke birnin Abuja ya samu gagarumar kyauta da za ta inganta da kuma kawo ci gaba ga Musulunci
  • Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Aminu Baba-Kusa shi ya ba da wannan gudunmawa ta makeken fili ga masallacin
  • Baba-Kusa ya ce ya yi wannan kyautar ce don ba da ta shi gudunmawa wurin inganta tare da fadada addinin Musulunci

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Wani shahararren dan kasuwa kuma mai taimakon al’umma ya bai wa masallacin Al-Noor da ke Abuja kyautar makeken fili.

Dan kasuwar mai suna Alhaji Aminu Baba-Kusa ya ce ya ba da gudunmawar ce don Allah da kuma taimakon Musulunci.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi dalilin da ya sa ya kamata CBN ta dakatar da amfani da sabbin kudi

Dan kasuwar Arewa ya ba da gudunmawar makeken fili ga masallacin Al-Noor
Wani dan kasuwa ya ba da gudunmawar fili ga masallacin Abuja. Hoto: VON.
Asali: UGC

Mene dalilin ba da kyautar filin ga masallacin?

Masallacin Al-Noor da ke Abuja na karkashin Cibiyar Inganta Addinin Musulunci (ICICE), cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baba-Kusa ya ce hakan zai kara fadada Musulunci a birnin Tarayya Abuja da kuma kasa baki daya.

Dan kasuwar ya mika takardun filin ne ga shugaban kwamitin amintattu na cibiyar, Farfesa Ibrahim Sulaiman tare da rakiyar ma’akatan wurin.

Ya ce:

“Mun yanke shawarar kyautar da rabin filin da ke kewaye da masallacin Al-Noor ga Cibiyar Inganta Addinin Musulunci (ICICE).”

Wane martani ma su gudanar da masallacin su ka yi?

Ya kara da cewa ya na da tabbacin cibiyar za ta ci gaba da yada koyar da addinin Musulunci a kasar baki daya, Muslim Voice ta tattaro.

Babban daraktan ICICE, Dakta Kabir Kabo Usman ya ce wannan cibiya za ta ci gaba da inganta Musulunci tare da goyon bayan Bankin Raya Musulunci da wasu ma su taimakon cibiyar.

Kara karanta wannan

Hawan jini ya 'kashe' mutane da aka tsige ‘Dan majalisar da ya ci kuri’u 95, 000

Ya ce:

“Wannan zai kara ba mu damar cimma burukanmu da mu ka saka a gaba na kirkirar Jami’ar Al-Noor a Abuja. “

Masallacin Abuja ya tara biliyan 1.3

A wani labarin, Cibiyar Inganta Addinin Musulunci (ICICE) ta ce masallacin Al-Noor ya tara fiye da naira biliyan 1.3 domin fadada masallacin.

Daraktan cibiyar, Dakta Kabir Kabo shi ya bayyana haka inda ya ce za su fadada masallacin mai cin mutane dubu 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.