Kaya Za Su Kara Tsada a Sakamakon Canjin Kudin da Kwastam Tayi wa ‘Yan Kasuwa

Kaya Za Su Kara Tsada a Sakamakon Canjin Kudin da Kwastam Tayi wa ‘Yan Kasuwa

  • Kwastam ta kasa ta canza lissafin da ta ke amfani da shi wajen karbar kudin shigo da kaya daga kasashen ketare
  • A maimakon N770.88/$, Hukumar ta canza farashin Dala zuwa N783 wanda tabbas zai shafi kudin kaya a Najeriya
  • Abin da ya jawo hakan shi ne karya farashin Naira da babban bankin CBN ya yi bayan Bola Tinubu ya hau kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Watanni kusan biyar da bankin CBN ya canza tsari, ya saki farashin Naira ga 'yan kasuwa, hukumar kwastam ta canza lissafinta.

The Guardian ta ce a yanzu hukumar kwastam ta kasa ta daidaita farashin kudin shigo da kaya kasar daga N770.88/$ zuwa N783.174/$.

'Yan kasuwa
Kaya daga ketare za su shigo kasuwa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kwastam ta canzawa 'yan kasuwa kudin shigo da kaya

Kara karanta wannan

Kudin litar man Fetur zai iya saukowa saboda faduwar farashin ganga a Duniya

Canjin ya nuna a shafin hukumar ta kwastam wanda ‘yan kasuwa su ka tabbatar da cewa hakan zai shafi yadda ake shigo da kayayyaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauyin zai yi sanadiyyar canza kudin da ake karba wajen shigo da kaya Najeriya daga kasashen waje, watakila farashi su kara tsada.

Yadda 'yan kasuwa su ke jin jiki a Najeriya

Da sabon farashin na N783.174/$ za a rika amfani idan za a biya kudin kayan waje da aka kawo, a karshe za a ga tasirin canjin a kasuwa.

Tun kafin yanzu, rahoton ya ce kayan da ake shigowa da su daga ketare sun ragu da kusan 70% saboda tsare-tsaren CBN da na gwamnati.

Tashin kudin kasar waje da haraji ya na wahalar da ‘yan kasuwa, sannan farashin sufuri ya karu a dalilin tsadar dizil da cire tallafin fetur.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

Kasuwanci ya fi sauki a sauran kasashe

Kudin da gwamnatin Najeriya ta ke karba idan mutum ya shigo da kaya ta jirage ya zarce abin da ake karba a sauran kasashen da ke Afrika.

Kamar yadda Adegboyega Oyetola ya fada, akwai kayan da sun yi shekaru sama da 10 a ajiye saboda irin wahalar da ‘yan kasuwa su ke sha.

Saboda haka wasu su ke kai kayansu kasashe irinsu Ghana, Togo da Kamaru, a sauke a can domin tsadar su ba ta kama hanyar Najeriya ba.

Najeriya ta hada-kai da Saudi

Wani rahoto da mu ka fitar dazu ya nuna an shiga MoU da za ta taimaki Najeriya wajen hako mai da samun kudin shiga da kuma kawo ayyukan yi.

Karamin ministan mai ya ce daya daga cikin muhimman amfanin fitacciyar yarjejeniyar da aka shiga da Saudi ita ce za ta taimaka da fasaha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng