Gwamna Radda Na Katsina Ya Bayyana Matakin Dauka Bayan Ƴan Bindiga Sun Dawo Kai Hare-Hare a Jiharsa
- Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya nuna takaicinsa kan asarar rayukan da aka yi a jihar saboda hare-haren ƴan bindiga
- Gwamna Radda ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da al'ummar jihar baki ɗaya
- Dikko Radda ya kuma sha alwashin murƙushe ƴan bindigan da ke aikata ayyukan ta'addanci a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi Allah-wadai da hare-hare da kashe-kashen rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a wasu sassan jihar da ƴan bindiga suka yi cikin ƴan kwanakin nan.
Gwamna Radda ya kuma sha alwashin murƙushe ƴan bindiga ta yadda jihar za ta gagare su zama a cikinta, cewar rahoton The Punch.
Gwamnan ya yi wannan alƙawarin ne a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar, Bala Salisu-Zango ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya yi tir da hare-haren ƴan bindiga
Salisu-Zango ya bayyana cewa, Radda ya yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a ƙananan hukumomin Musawa, Danmusa, Matazu, da Faskari na jihar.
Ya ce, Radda ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje da ta'aziyya a garin Musawa, inda ƴan bindigar suka kashe kimanin mutum 17 a wajen taron Mauludi.
"Na yi matuƙar kaɗuwa da yadda miyagu da ƴan bindiga marasa imani ke kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a wasu ƙauyukan mu." A cewarsa.
Wane alwashi gwamnan ya sha?
Ya nanata aniyar gwamnatinsa ta fatattakar ƴan bindigan a maɓoyarsu tare da jajanta wa mazauna yankunan da abin ya shafa da suka rasa ƴan uwansu.
"Bari na yi amfani da wannan dama domin in jajanta wa al'ummar waɗannan ƙauyukan, da iyalan waɗanda abin ya shafa, da kuma al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya bisa asarar da aka yi." A cewar Radda.
Ya bayyana cewa, a makonnin da suka gabata, jami’an hukumar tsaron jihar da aka kafa a jihar sun fatattaki ƴan bindiga da dama a maɓoyarsu a faɗin jihar.
Ya ce hakan ya sanya ƴan bindigan suka riƙa shirya kai hare-haren ramuwar gayya.
Wani mazaunin jihar Katsina mai suna Ibrahim Sanusi ya gaya wa wakilin Legit Hausa cewa matsalar tsaro ta kusa zuwa ƙarshe a jihar Katsina da yardar Allah.
Ibrahim ya yaba da ƙokarin da Gwamna Dikko Radda yake yi wajen shawo kan matsalar tsaron da ta daɗe tana addabar jihar.
Ya yi nuni da cewa tun bayan hawan gwamnan kan karagar mulki ya ɗauki matakai domin magance matsalar tsaro a jihar.
Ƴan Bindiga Sun Tafka Illa a Katsina
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, ta bayyana illar da ƴan bindiga suka yi wa jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa aƙalla makarantu 123 aka rufe gaba ɗaya sannan cibiyoyin kiwon lafiya sun kai 58 waɗanda suka daina aiki gaba ɗaya a jihar saboda ayyukan ƴan bindiga.
Asali: Legit.ng