Kano: Kotun Musulunci Ta Umurci Magidanci Ya Karbi Ɗan Da Ya Ke Kokwanton Ba Nasa Bane

Kano: Kotun Musulunci Ta Umurci Magidanci Ya Karbi Ɗan Da Ya Ke Kokwanton Ba Nasa Bane

  • An samu takaddama mai zafi tsakanin wani magidanci da tsohuwar matarsa a wata kotun shari'a da ke Kano, bayan matar ta haihu kuma ta ce dan na shi ne
  • Sai dai magidancin ya ki karbar yaron, yana ikirarin dan da ta haifa ba nashi bane, sakamakon gwajin da aka yi a asibiti tun bayan kwanaki 16 da zuwanta gidansa
  • Sai dai alkali, Khadi Abdullahi, ya ba mutumin umurnin karbar yaron kasancewar ya gaza kawo hujjar ganin matar da wani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Kano, ta bai wa wani mutum mai suna Mudassir Adamu mazaunin Sheka Quarters dansa bayan da aka samu rashin jituwa tsakaninsa da matarsa ​​da suka rabu kan wanda zai rike yaron.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai cigaba da biyan tallafi, ya ki yarda a kara kudin wutar lantarki

Khadi, Abdullahi Halliru Abubakar, ya bayyana cewa mutumin ba shi da dalilin kin karbar yaron tunda ya taba auren matar.

Kotun Kano
Mai shari'a ya umurci magidancin ya karbi yaron, saboda gaza kawo hujjar da za ta nuna yaron ba nashi ba ne Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Dalilin da yasa ba zan karbi yaron ba - Mudassir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko dai, magidancin ya yi jayayya kan cewa ya zauna da tsohuwar matarsa ​​ne na tsawon kwanaki 16, kuma a lokacin da suke tare, ta yi ikirarin cewa tana da ciki amma bayan gwajin da aka yi a asibiti, an tabbatar ba ta dauke da juna biyu.

Ya kara da cewa wani ya shaida masa cewa cikin ba nasa ba ne, kuma wani daga gidansu matar ya ce ta tabbatar masa da cewa ta jinin al'adarta har sau biyu bayan rabuwarsu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Hukuncin da kotu ta yanke

A nata bangaren, matar da aka saki, Fatima Aminu Umar, kuma mazauniyar Sheka Quarters, ta yi ikirarin cewa sun shafe makonni biyar da yin aure kuma ta haihu bayan shekara guda.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

Khadi Abubakar ya bada umarnin a mayar da yaron wurin tsohon mijin, tunda ya kasa kawo hujjar ganinta da wani.

Rashin haihuwa, wata mata ta bukaci a datse igiyar aurenta

A wani labarin, wata matar aure, Shakirat Ayinla a ranar Alhamis, ta roki kotun kwastomare da ke da zama a Centre-Igboro Ilorin, jihar Kwara, ta datse igiyar aurenta, bisa dalilin da ta bayar na cewar ita da mijin sun kwashe shekaru biyu ba tare da haihuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.