"Babu Wanda Ya Tsira": Mutum-Mutumi Ya Samu Tangarda, Ya Kashe Ma'aikaci Kafin a Farga

"Babu Wanda Ya Tsira": Mutum-Mutumi Ya Samu Tangarda, Ya Kashe Ma'aikaci Kafin a Farga

  • A wani mummunan al'amari da ya afku, mutum-mutumi ya kashe wani mutum a wata masana'antar sarrafa barkono a Koriya ta Kudu
  • Mutumin na kula da ayyukan na'urar mutum-mutumin ne kafin gwaji kwatsam sai al'amarin ya afku
  • Wannan ba shine karo na farko da mutum-mutumi ke ji wa mutum ciwo ko yin kisa ba a Koriya ta kudu yayin da kwararru da dama suka yi korafi

Mutum-mutumi ya kashe wani mutum a ata masana'antar sarrafa barkono a Koriya ta Kudu bayan ya yi kuskuren daukar shi a matsayin kwalin kayan lambu, kamar yadda BBC ta rahoto.

Wanda abun ya ritsa da shi, ma'aikacin kamfanin dillancin mutum-mutumi wanda ke ganiyar shekaru 40, yana cikin kula da ayyukan na'urar mutum-mutumin a daren ranar Laraba, lokacin da na'urar ta kama shi tare da rusa masa fuska da kirji.

Kara karanta wannan

An Kama Mutane 4 Kan Laifin Satar Kujerar Bandaki Na Gwal Daga Fadar Blenheim

Mutum-mutumi ya halaka wani ma'aikaci
Yadda Mutum-Mutumi Ya Taushe Ma’aikacin Kamfani Har Lahira, Cikakken Bayani Ya Bayyana
Asali: Facebook

An kwashe shi zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa

An kera mutum-mutumin ne don daukar kwalayen barkono da tura su zuwa inda za a nika su. Mutumin na ta duba na'urar gabannin gwajin da za a yi a ranar Juma'a, amma sai mutum-mutumin ya samu matsala sannan ya gaza banbance shi da kwalayuen, kamfanin ya rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya afku ne a rukunin gonaki na Donggoseong Export da ke lardin Gyeongsang ta Kudu, wanda yake mallaki masana'antar.

Wani jami'in kamfanin ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin sannan ya yi kira da a samar da tsarin daidaitawa da bayar da kariya.

Mutum-mutumi ya saba barna a Koriya ta kudu

Wannan ba shine karo na farko da mutum-mutumi ke raunata mutum ko aikata kisa ba a Koriya ta kudu.

A watan Maris, wani mutum mai shekaru 50 ya samu munanan rauni bayan da wani mutum-mutumi ya murkushe shi lokacin da yake aiki a wata masana'antar kera kayayyakin mota.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 20, jerin sunaye

Wasu masana sun yi gargadin kan illar da ke tattare da na’urar mutum-mutumi a yayin da suke samun ci gaba da cin gashin kansu.

A shekarar 2017, gungun masu bincike na sirri da masu ilimin dabi'a sun fitar da wata budaddiyar wasika inda suka yi kira da a hana amfani da makamai masu cin gashin kansu, ko "mutum-mutumi masu kisa", wadanda za su iya kai hari ba tare da sa hannun dan Adam ba.

Sun bayyana cewa irin wadannan makamai za su zama barazana ga tsaro da kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, kuma za su iya haifar da wata sabuwar nau'in makamai.

Mutum-mutumi na ba da hannu a Abuja

A wani labari, mun ji cewa an gano wani mutum-mutumi yana ba da hannu a wani titin Abuja mai cike da cunkoson ababen hawa.

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya, an gano mutum-mutumin da ke tsaya a tashar yan sanda kan hanyar inda yake ba ababen hawa hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng