Yanzu: Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Karin N2.17trn a Kasafin Kudin 2023

Yanzu: Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Karin N2.17trn a Kasafin Kudin 2023

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan karin kasafin kudin 2023 wanda yake kan naira triliyan 2.17
  • Tinubu ya rattaba hannu kan takardar kasafin kudin ne a yau Laraba, 8 ga watan Nuwamba a fadar Villa
  • Hakan ya biyo bayan amincewar da ya samu daga majalisun tarayya bayan kasafin kudin ya tsallake karatu na uku

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan karin naira tiriliyan 2.17 na kasafin kudin 2023.

Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Tinubu ya sanya hannun ne a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da karin kasafin kudin 2023 na N2.17trn bayan tsallake karatu na uku.

Kara karanta wannan

FG ta kashe biliyan 90 kan tafiye-tafiyen Shugaban Kasa cikin shekara 9, Sabon Bincike

Shugaban kasa Tinubu ya rattaba hannu a karin kasafin kudin 2023
Yanzu: Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Karin N2.17trn a Kasafin Kudin 2023 Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Kafin aiwatar da kudurin, majalisar dattawa ta amince da rahoton zaman da aka yi tsakanin majalisun biyu kan karin kasafin kudin 2023 kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kudi, Sanata Solomon Olamilekan Adeola ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudirin ya yi hanzarin tsallake karatu a majalisun tarayya kamar yadda yan majalisar suka ce don amfani kasa ne.

Tinubu dai ya aika sako majalisa inda ya nemi ta amince da N2,176,791,286,033 a matsayin karin kasafin kudin 2023 don magance karin albashin ma'aikata, tsaro da sauransu, rahoton Channels TV.

Shugaban kasar ya kuma aike da tsarin kashe kudi na MTEF na 2024-2026 zuwa majalisun tarayya.

Tafiye-tafiyen shugaban kasa ya lakume N90bn

A wani labarin, mun ji cewa batu kan irin makudan kudaden da ake ware wa bangaren tafiye tafiyen shugaban kasa a jiragen sama ya fara tayar da hazo, inda cikin shekaru tara aka kashe akalla naira biliyan 90 kan sufurin shugaban kasa a jirgin sama.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Za a Gudanar da zanga-zangar kwana 30 har sai Tinubu ya yi murabus

Kara yawan kudin a cikin kasafin kudin kasa ya jawo muhawara mai zaifi, da ya kai ga har an fara bin ba'asin sanin manufar gwamnati kan kudaden da ake kashewa a kasar, da kuma sanin abin da ta ke yi na alkinta kudaden jama'a.

Misali, a shekaru hudun farko na tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, an ware naira biliyan 20.42 don sufurin shugaban kasar a jirgi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel