Akarshe, EFCC Ta Bi Umarnin Kotu Kan Ci Gaba da Rike Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele

Akarshe, EFCC Ta Bi Umarnin Kotu Kan Ci Gaba da Rike Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele

  • A karshe, hukumar EFCC ta bi umarnin kotun wurin mika Emefiele a gabanta a yau Laraba 8 ga watan Nuwamba
  • A ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba kotun ta umarci hukumar ta yaki da cin hanci da ta sake shi ko ta mika shi gabanta
  • Wannan na zuwa ne bayan sake Emefiele da DSS su ka yi a makon jiya kafin EFCC kuma su sake nade shi a Abuja

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hukumar EFCC ta gabatar da tsohon shugaban CBN, Godwin Emefiele a gaban kotu don ci gaba da sauraran shari’a kan ba da belinsa.

Kotun wacce ke zamanta a birnin Abuja ta umarci hukumar EFCC da ta sake Emefiele ko ta tabbatar ta mika shi gabanta.

Kara karanta wannan

Emefiele: Kotu ta cimma matsaya kan tsohon gwamnan CBN bayan mika shi da EFCC ta yi

Kotu ta ba da belin tsohon gwamnan CBN, Emefiele
Hukumar EFCC ta mika Emefiele kotu. Hoto: Legit.
Asali: UGC

Yaushe hukumar EFCC ta mika Emefiele ga kotun?

Hukumar ta EFCC ta mika Emefiele ne a yau Laraba 8 ga watan Nuwamba a babbar kotun da ke Abuja, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rike Emefiele bayan dakatar da shi daga gwamnan babban bankin CBN.

A makon da ya gabata, hukumar DSS ta sake Emefiele inda awanni kadan da sake shi, hukumar EFCC ta sake nade shi saboda korafe-korafen da ke kansa.

Wasu korafe-korafe ne ake zargin Emefiele a kai?

Ana zargin Godwin Emefiele da badakalar makudan kudade yayin da ya ke kan kujerar gwamnan CBN, cewar Nairametrics.

Har ila yau, akwai korafe-korafe kan Emefiele na zargin daukar nauyin ta'addanci a wanda ya jawo rasa rayuka..

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele kan zarge-zarge da ake yi masa tun farkon hawanshi mulki a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Kisan Janar Alkali: An samu ci gaba yayin da lauyan mai kara ya gabatar da muhimmiyar shaida

Kotu ta ba da belin Emefiele

A wani labarin, babbar kotun Tarayya ta ba da belin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele bayan mika shi da EFCC ta yi.

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Adeniyi ya umarci Gwamnatin Tarayya da ta sake Emefiele ga lauyoyinsa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rike tsohon gwamnan CBN din kan wasu korafe-korafe da ake yi a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.