Dawowar Harin Boko Haram a Wasu Jihohi Ya Tada Hankalin ‘Yan Majalisan Tarayya

Dawowar Harin Boko Haram a Wasu Jihohi Ya Tada Hankalin ‘Yan Majalisan Tarayya

  • A majalisar wakilan tarayya, an tattauna game da sababbin hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai kwanan nan
  • An rasa mutane da-dama a wasu kauyukan Yobe da Borno a lokacin da ake tunanin an ci karfin ‘yan ta’addan tun tuni
  • ‘Yan majalisar tarayya sun bukaci jami’an tsaro su tashi-tsaye, sannan an yi kira ga gwamnati da ta kai wa mutane agaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - ‘Yan majalisar wakilan tarayya da ke wakiltar jihohin Borno da Yobe sun nuna damuwarsu a game da dawowar ‘yan Boko Haram.

A rahoton Tribune, an fahimci cewa ‘yan majalisar wadannan jihohi biyu sun yi magana game da bukatar kare rayuwa da dukiyoyin jama’a.

A karshen zaman da aka yi a ranar Talata, majalisar wakilai ta amince da bukatar da aka gabatar na kai agajin sojoji na gaggawa a yankunan.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa wani harsashi har lahira yayin gwada maganin bindiga a Bauchi

‘Yan Majalisan Tarayya
'Yan Majalisa sun yi maganar Boko Haram Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Sababbin hare-haren Boko Haram

Majalisa ta ce ya kamata jami’an tsaro su ceto manoman nan da aka yi awon gaba da su a garuruwan Koshebe, Karkut da Bulabilin da ke Jere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ahmed Satomi ya ce ‘Yan ta’addan na kungiyar Boko Haram sun shiga garin Jere a karamar hukumar Mafa a jihar Borno kwanakin baya.

Haka zalika Hon. Shettima Ali ya shaidawa majalisa cewa an kai hari a wasu kauyukan karamar hukumar Geidam, aka dauke Bayin Allah.

'Yan Boko Haram suna daf da Maiduguri

Punch ta ce Hon. Satomi ya nemi majalisa ta sa baki a ceci mutanen mazabarsa, ya ce inda aka kai hari kilomita 20 ne zuwa birnin Maiduguri.

‘Dan majalisar ya ce ‘yan ta’addan sun kirkiro wata dabara na hawa babura, sai sur aba kansu, su na kai hari ne yanzu da adduna da wukake.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Majalisar ta lura cewa kungiyoyin dakarun sa-kai a Arewa maso gabashin Borno sun gano gawawwaki 9 kuma ana neman sauran da aka rasa.

Boko Haram: Majalisa ta dauki matsaya

Majalisa ta damu da cewa duk da harin da aka kai ranar 4 ga watan Nuwamba, an sake yi wa mutane 50 kisan gilla a ranar Lahadi 5 ga wata.

Shugaban majalisa, Tajudeen Abbas, ya gamsu da kiran da aka yi na cewa jami’an NEMA, NEDC da sauransu, su kai wa mutanen yankin agaji.

"Babu Boko Haram a nan"

Legit ta tattauna da wani mazaunin Damaturu a jihar Yobe, Muhammad Adamu, wanda ya shaida mata hare-haren ba su kai gare su ba.

Muhammad Adamu yake cewa 'yan ta'addan suna kai hari ne a kauyukan Arewa maso gabas, a cewarsa ba a shigo manyan birane ba.

A cewarsa ko kwanaki da aka hallaka mutane a Geidam ne da ke nesa da su, akalla kilomita 200 da babban birnin Yobe watau Damaturu.

Kara karanta wannan

Babu maganar komawa Majalisa bayan Ministar Tinubu ta fado ta kai a Kotun zabe

Israila ta kashe dubban Falasdinawa

A kasar waje, an ji labari Benjamin Netanyahu ya ce babu maganar tsagaita wuta a Falasdinu ba tare da an dawo da ribatattun kasar Israila ba.

A game da tsaida yaki da Hamas, a matsayinsa na Firayin Ministan Israila, Netanyahu ya ce ba su da mafita dabam da luguden wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng