Isra’ila vs Hamas: A Karshe, Majalisa Ta Yi Martani Kan Rikicin, Ta Tura Muhimmin Sako Ga MDD

Isra’ila vs Hamas: A Karshe, Majalisa Ta Yi Martani Kan Rikicin, Ta Tura Muhimmin Sako Ga MDD

  • Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, Majalisar Dattawa ta yi martani kan matsalar
  • Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi shi ya kawo wannan kuduri a yau Talata 7 ga watan Nuwamba a dakin Majalisar
  • Mambobin Majalisar da dama sun ba da gudunmawa inda su ka yi Allah wadai da kasha-kashen al’umma a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawa ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta yi kokarin kawo karshen rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas.

Majalisar ta bayyana haka ne a yau Talata 7 ga watan Nuwamba yayin zamanta a birnin Tarayya Abuja, cewar Vanguard.

Majalisar Dattawa ta yi martani kan rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas
Majalisa ta yi martani kan rikicin Isra'ila da Hamas. Hoto: NASS TV.
Asali: Facebook

Wane bukata Majalisar ta tura ga kan rikicin?

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Har ila yau, Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani don kawo karshen rikicin a tsakanin kasashen biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta yi wannan kira ne yayin da dubban mutane da su ka hada da mata da yara da kuma ma’aikata ke rasa rayukansu a kullum.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas a yankin, cewar The Nation.

Wanene ya kawo kudurin kan rikicin?

Wannan na cikin wani kuduri da Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya kuma dan jam’iyyar PDP ya gabatar a gaban majalisar.

Aliero ya ce yawan mutanen da ke rasa rayukansu a rikicin ya wuce tunani inda ya ce idan ba a kawo karshen shi ba zai iya jawo yakin duniya na uku.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Za a Gudanar da zanga-zangar kwana 30 har sai Tinubu ya yi murabus

Sauran Sanatoci da su ka ba da gudunmawa a kudirin sun hada da Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano da Enyinnaya Abaribe na jihar Abia sai Sani Musa daga jihar Neja.

Hausa Legit ta ji ta bakin wasu kan wannan kuduri na Majalisar:

Isma'il Musa ya ce:

"A gaskiya ya kamata su fara dakile matsalar tsaro a gida kafin magana kan wasu kasashe."

Ibrahim Musa ya ce tabbas Majalisar ta yi abin da ya dace kuma hakan ya nuna su na kishinmu.

Ibrahim Muhd ya ce:

"Ai idan Najeriya ta saka baki a rikici to ya zo karshe, da ta saka baki a rikicin Rasha da Ukraine shi ma haka ya wuce."

Kasashen da ke tare da Isra'ila

A wani labarin, yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, kasashe da dama sun bayyana matsayarsu.

Wannan rahoto zai jero mu ku kasashen da ke goyon bayan Isra'ila da wadanda ke tare da Falasdinu da kuma 'yan ba ruwa na.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.