Matawalle Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Zamfara Ke 'Kulla Masa Makirci'
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Bello Matawalle ya kare kansa daga zarge-zargen da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ke yi masa
- Gwamna Dauda ya na zargin Matawalle da sama da fadi da makudan kudaden jihar da kuma wasu laifukan da suka shafi rashawa
- Sai dai a martanin da Matawalle ya yi wa gwamnatin Zamfara, ya ce Dauda na kulla masa sharri ne kawai don a cire shi daga kujerar ministan tsaro
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Bello Matawalle, karamin ministan tsaron, ya yi martani kan zarge-zargen rashawa da gwamnan Zamfara na yanzu ke yi masa.
Matawalle ya kasance gwamnan jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023, kuma ya rasa tazarcensa a zaben gwamnan jihar da aka gudanar, inda ya sha kaye a hannun Dauda Lawal na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
A baya bayan nan, gwamnan jihar Zamfara ya zargi Matawalle da yin sama da fadi da biliyoyin naira daga kudin ginin tashar jirgin saman daukar kaya na jihar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar ta zargi tsohon gwamnan da ba ma'aikatar kananan hukumomi umurnin cire naira biliyan daya daga asusun hadaka na kananan hukumomi a ranar 25 ga watan Oktoba, sannan ya biya naira miliyan 825 ga 'yan kwangilar da za su yi aikin ba tare da an yi aikin ba.
Gwamnan jihar ya kuma zargi Matawalle da bada izinin biyan kaso 100 na sama da naira biliyan daya don yin katanga, fitar da taswira da kuma yin kwaskwarima ga gidajen zaman gwamna da ke kananan hukumomi 14 na jihar.
An kuma zargi tsohon gwamnan da wasu laifukan da suka shafi rashawa.
Martanin Matawalle kan zarge-zargen da ake masa
Da ya ke zanta wa da wakilin DCL Hausa, tsohon gwamnan Zamfara ya zargi Lawal da daukar nauyin kulla masa sharri, inda ya ce ba a gwamnatinsa ne matsalolin jihar suka fara ba.
Matawalle ya yi ikirarin cewa dukkanin zarge-zargen da gwamnatin Zamfara ke yi masa yanzu ba gaskiya ba ne, kawai yana yi ne don kitsa makarcin cire shi daga minista.
Tsohon gwamnan ya kuma zargi Lawal da lalata duk wasu ayyuka da yayi a jihar don kawai ya kunyatar da shi, da nuna wa duniya kamar bai yi aikin komai a lokacin da ya ke gwamna ba.
Matawalle ya soki Dauda Lawal kan matsalar tsaro a Zamfara
A wani labarin makamancin wannan, Matawalle ya ce ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa kullum karuwa su ke a jihar Zamfara musamman a birnin Gusau.
Gwamnan ya ce hakan bai rasa nasaba da rashin kulawa na Gwamna Dauda Lawal Dare a bangaren samar da tsaro ga al’umma, Legit Hausa ta ruwaito
Matawalle ya bayyana haka ne yayin ganawa da Kungiyar ‘Yan Jaridu (NUJ) reshen jihar Zamfara a Abuja, TVC News ta tattaro.
Kotu ta tabbatar da nasarar Lawal Dare
Kazalika, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a jihar Zamfara ta tabbatar da Lawal Dare a matsayin sahihin wanda ya lashe zabe.
Kotun wacce ke zamanta a jihar Sokoto ta yanke hukuncin ne a yau Litinin 18 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng