NSCDC Ta Cafke Wata Mata Da Zargin Damfarar Gidan Marayu Miliyan 1, an Binciko Wasu Abubuwa
- Dubun wata mata ta cika bayan cafke ta da aka yi kan zargin damfarar gidan marayu makudan kudade a jihar Ekiti
- Matar mai suna Folasade mai shekaru 38 an cafke ta ne bayan gudanar da bincike inda aka gano ta damfari gidan marayun miliyan daya
- Kwamandan hukumar NSCDC, Olatunde Fayemi shi ya tabbatar da haka a jiya Litinin 6 ga Nuwamba yayin gurfanar da Folasade
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ekiti - Rundunar hukumar NSCDC ta cafke wata mata da ta damfari gidan marayu miliyan daya a jihar Ekiti.
Wacce ake zargin Folasade mai shekaru 38 ta kasance ma'aikaciya a gidan marayun inda ta karbi kudade ba tare da sanin su ba, Daily Post ta tattaro.
Mene hukumar NSCDC ke zargin matar a kai?
Kwamandan hukumar NSCDC a jihar, Olatunde Fayemi shi ya tabbatar da haka yayin gurfanar da ita da wasu masu laifi a jiya Litinin 6 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fayemi ya ce Folasade ta karbi makudan kudade a madadin gidan marayun ba tare da sanin su ba inda ta yi sama da fadi da su, cewar Tribune.
Kakakin hukumar a jihar, Afolabi Tolulope ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa inda ta ce matar ta karbi kudaden da wasu bayin Allah su ka kawo don taimaka wa yaran da su ke gidan.
Mene martanin NSCDC kan matar?
Ya ce:
"Ana kuma zargin Folasade da kwasar wasu kayayyaki zuwa gidanta wadanda aka kawo taimako ga marayun.
"Yayin gudanar da bincike, an binciki bayanai daga asusun bankinta inda aka gano ta shafe watanni tara ta na wannan badakalar.
An cafke matar da ta watsa wa mijinta man gyada
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Ribas sun cafke wata mata da zargin watsa wa mijinta tafasasshen man gyada.
Matar da ake zargi mai suna Hope ta shammaci mijin ne yayin da ya ke bacci inda ta ma sa wanka da man gyadar.
Yayin da ya ke martani, mijin ya ce wata 'yar hatsaniya ce ta shiga tsakaninsu wanda bai taba zaton zai kai ga haka ba.
Asali: Legit.ng