Wani mutumi yayi da'awar Annabta a Kasar Sudan

Wani mutumi yayi da'awar Annabta a Kasar Sudan

- Wani mutumi yace shi Annabi ne kuma ana yi masa wahayi

- Wannan mutumi ya fito ne daga Yankin Darfur ta kasar Sudan

- Har da ma wata sura yace an sauke masa ga mutanen sa

Wani mutumi mai suna Abdulwahid Muhammad Nur a can kasar Sudan yace wai shi ma Annabin Allah ne kuma Ubangiji ya turo sa ga mutanen sa.

Wani mutumi yayi da'awar Annabta a Kasar Sudan
Wasu Mutanen Kasar Sudan

Wannan dan banza yace ana yi masa wahayi kamar dai Annabawan Allah kuma tuni har an sauko masa da wata Sura mai suna Sural Darfur watau ta mutanen Garin Darfur da ke Kasar Sudan.

KU KARANTA: An shiryawa Matan Chibok liyafa

A surar dai kamar yadda mu ka ji yana karanta ta, an ambaci mutanen na sa da ma na Nahiyar Afrika da kuma shi karen kan sa wannan mutumi a ayoyin. Wannan mutumi dai yace Ubangiji ne ya aiko sa domin ya gargadi Jama'a daga azaba.

A hudubar Juma'ar wannan makon, wani Malami a Zaria yayi kira ga Jama'ar kasar su gyara mu'amalar su tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Su wa su ka fi yaudara a zaman aure?

Asali: Legit.ng

Online view pixel