Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar

Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar

- Majalisar Malaman Addinin Musulunci a Najeriya ta nemi Gwamna Abdullahi Ganduje da ya sassautawa Sheikh Abduljabbar Kabara

- Kungiyar ta bukaci da ya sake bude masallacin Shehin Malamin domin gudanar da ayyukansa na yau da kullun

- Ta ce hakan ne zai zamo adalci kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta ba kowani dan kasa yancin yin addininsa

Majalisar Malamai ta Najeriya, karkashin inuwar kungiyar Malaman Addinin Musulunci a Najeriya ta yi kira ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Ta nemi da ya dage takunkumin da ya sanya wa malamin nan, Sheikh Abduljabbar Kabara tare da sake bude masallacinsa domin gudanar da ayyukansa na yau da kullun, Vanguard ta ruwaito.

Ku tuna cewa a watan da ya gabata, Ganduje ya hana Abduljabbar yin wa’azi da gabatar da Sallah a masallacinsa sakamakon zarge-zargen da wasu malaman addinin Islama ke yi a jihar.

Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar
Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya ya bayyana dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar mulki

Da yake jawabi ga manema labarai a gidansa da ke Bauchi a ranar Alhamis, Mukaddashin Shugaban Majalisar na kasa wanda ya zamo shugaban darikar Tijjaniya, Sheikh Dan’azumi Tafawa Balewa ya ce dakatar da Sheikh din da aka yi wani lamari ne da ke damun majalisar.

Ya ce don tabbatar da adalci da kuma bin kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya ba kowane dan kasa ‘yancin yin addini, ya kamata gwamna Ganduje ya kyale Sheikh Abduljabbar ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullun.

Da take kawo misalai daban-daban a cikin tarihin Musulunci inda aka warware rashin jituwa ta hanyar tattaunawa.

Majalisar wacce aka kafa a 1980 ta ce tana dauke da dukkanin mazhabobi da kungiyoyi daban-daban masu rikitarwa na Musulunci da nufin samar da hadin kai ta hanyar ra'ayi daban-daban.

"Wannan hakki wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar yana cikin cikakkiyar yarjejeniya tare da umarnin Alkur'ani mai girma wanda Allah yake cewa 'Babu tilastawa a cikin addini.

"Muna mutunta ra'ayoyi masu karo da juna kuma a shirye muke mu inganta tattaunawa da fahimtar juna tsakanin dukkanin kungiyoyin Musulmi masu rikici," in ji shi.

Sheikh Dan Azimi wanda ya koka kan dakatar da tattaunawar da aka shirya da kotu ta yi, wanda a baya Gwamna Ganduje ya shirya tsakanin Abduljabbar da sauran malamai.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano

Ya bayyana cewa idan har za a bar masu adawa da Abduljabbar din su sami ‘yancinsu da kuma fadin albarkacin bakinsu, ya kamata a ba Sheikh Abduljabbar irin wannan damar.

A baya mun ji cewa shugaban malamai na arewa maso yamma, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa kima da darajar Malam Abduljabbar Kabara basu kai ga malamai su yi masa gangamin taron dangi ba.

Sheikh Khalil ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da jaridar Leadership kan abinda ke faruwa tsakanin Abduljabbar da gwamnatin Kano.

Tun farko dai Ganduje ya haramtawa malamin yin wa'azi sakamakon zargin da da ake yi da bayar da wasu fatawoyi da suka sabawa koyarwar addini.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel