Bidiyon Wani Mutum da Ya Juye Galan Din Man Ja a Injin Mota Ya Girgiza Intanet
- Bidiyon wani mutum da ya zuba man ja a injin din mota ya yadu kuma ya ba mutane da dama mamaki
- A bidiyon, wanda ya yadu a TikTok, an gano inda mutumin ya yuje galan din man ja a injin din, wanda ke nuna yana so ya yi amfani da shi a matsayin man injin
- Wasu mutane sun lura cewa man jan zai shafi injin din nan da yan watanni kuma cewa mai motar zai yi danasanin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jama'a sun yi cece-kuce a kan wani bidiyon TikTok da ya yadu wanda ke nuna yadda aka yi amfani da man ja a madadin man injin din mota.
A cikin dan gajeren bidiyon, mutumin ya juye galan din man ja a cikin injin din motar a wani wuri da ke kama da wajen gyaran motoci.
A cikin bidiyon wanda shafin @ricochoco25 ya wallafa, mutumin ya juye man jan a cikin injin din kamar dai yadda ake zuba man injin.
Wau mutane sun koka kan ci gaban, sannan suka gaggauta bayyana illart da wannan ka iya yi wa motar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, wasu mutane sun bayyana cewa za su gwada a nasu motocin don gabin abun da zai faru da injin din.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Korlynse ya ce:
"Ina ganin nine mutum na gaba da zan yi amfani da man ja a motata kirar Toyota."
@Nas ya yi martani:
"Duk wanda ya yarda da wannan makanikin ya zuba man ja a motarsa zai kasance cikin hawaye nan da yan watanni kadan."
@PURPOSE ta ce:
"Yanzu man ja da muke amfani da shi wajen girka wakenmu hankali kwance zai yi tsada."
@Tradesmart ya ce:
"Zuwa dan lokaci zai sa karfen ya yi tsatsa saboda kasancewar ruwa."
Motar da ake tukawa ta bai-bai
A wani labarin, wani fasihin mutum mai suna Rick Sullivan ya kirkiro wata mota wanda ba a taba ganin irin ta ba. Wannan ya faru ne a kasar Amurka.
Legit.ng tace Rick Sullivan ya kera wata mota da take tafiya a bai-bai. Wannan mutumi da makaniki ne, yace motar ba za ta taba shiga kasuwa ba.
Kamar yadda muka samu rahoto a ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021, Mista Rick Sullivan ya shafe tsawon wata da watanni yana aikin wannan mota.
Asali: Legit.ng