Karai-Karai: An Fassara Bibul Zuwa Harshen Gargajiya Na Yan Asalin Jihar Yobe
- Hukumar Fassarar Bibul a Najeriya, NBTT ta yi nasarar fassara littafin zuwa yaren Karai-karai don taimakawa al’umma sanin ubangiji
- Wannan aiki ta fassarar an yi ta ne da hadin gwiwar Kungiyar Yaren Karai-karai da ke jihar Yobe don inganta yaren a tsakanin al’umma
- Shugaban kungiyar KKBLA a jihar Yobe, Mista Yusuf Musa shi ya bayyana haka a Potiskum babban birnin jihar Yobe
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Yobe – Hukumar Fassara Bibul a Najeriya (NBTT) ta fassara littafin zuwa yaren Karai-karai da ke jihar Yobe.
Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda inganta yaren a tsakanin Kiristoci da ke fadin kasar, Legit ta tattaro.
Mene dalilin fassara Bibul zuwa yaren Karai-karai?
Aikin fassarar an yi ta ne da hadin gwiwar Kungiyar Yaren Karai-karai (KKBLA) don samun saukin fahimtar abin da ke kunshe a cikin Bibul.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar KKBLA a jihar Yobe, Mista Yusuf Musa shi ya bayyana haka a Potiskum babban birnin jihar Yobe.
Musa ya ce sun fara wannan gagarumin aiki ne tun a ranar 2 ga watan Agusta na shekarar 2005, cewar Daily Trust.
Wane shawara hukumar ta bayar kan yaren Karai-karai?
Ya ce aikin ya tsaya har na tsawon shekaru 23 kafin sakataren NBTT ya ziyarci jihar a shekarar don sanin ko su na da bukatar ci gaba fassarar.
Ya kara da cewa wannan fassara da aka yi ta Bibul zuwa yaren Karai-karai zai taimaka matuka wurin ci gaban yaren da kuma Kiristanci.
Hukumar NBTT ta samar da kwafin Bibul da aka fassara zuwa harshen Karai-karai akalla dubu 124 don taimakawa mutane fahimtar ubangiji.
Yayin da ya ke martani, daraktan NBTT, wanda ya samu wakilcin Patience Toma ya ce ya kamata ana koyar da yaren Karai-karai a makarantu.
Ya ce koyar da yaren a makarantu zai taimakawa yara rubutu da karatu da kuma sanin yadda za su bautawa ubangiji.
Babu Kalmar kirsimeti a Bibul
A wani labarin, Shahararrn Fasto mai suna Daniel Olukoya ya bayyana dalilin da ya sa ba sa bikin kirsimeti.
Ya ce sun dauki wannan matakin ne saboda a cikin Bibul babu wata kalmar da ta shafi bikin kirsimeti da Kiristoci ke yi.
Asali: Legit.ng