An kama wani faston da ya halasta zina da shan giya a Tanzania

An kama wani faston da ya halasta zina da shan giya a Tanzania

- Jami'an 'yan sanda sun kama faston da yace littafin injila ya halasta shan giya da zina a kasar Tanzaniya

- Yan sanda sun kama faston Manzo Tito a wurin shakatawa da shan giya

Jami’an ‘yan sandan kasar Tanzania sun kama wani Fasto mai suna, Onesmo Machibya wanda aka fi sani da Manzo Tito, akan wa’azin da yayi na cewa littafin injila ya halasta zina da shan giya.

Gwajin lafiyar da aka yi wa mutumin mai suna Onesmo Machibya, mai shekaru 44, , ya nuna cewa yana da tabin hankali, in ji Gilles Muroto, shugaban rundunar 'yan sanda a babban birnin kasar, Dodoma.

An kama wani faston da ya halasta zina da shan giya a Tanzania
An kama wani faston da ya halasta zina da shan giya a Tanzania

Har yanzu babu daya daga cikin wakilan Fasto Tito da yi magana akan wannan al’amari.

KU KARANTA : Muryar Amurka (VOA) ta fitar da fim din tarihin ta'adancin kungiyar Boko Haram a birnin New York

Wata bidiyo dake yawo a shafikan sada zumunta, ya nuna faston da ke ikrarin cewa shi manzo ne yana rawa kuma yana sumbatar matarsa da wata matashiya, yana mai cewa babu matsala mutum ya yi jima'i da matar da ba tasa ba

'Yan sanda sun kama shi ne a wani wurin shakatawa da sayar da kayan barasa a Dodoma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng