'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wurin Taron Mauludi a Katsina, Sun Halaka Mutum 20 Da Sace Wasu Da Dama

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wurin Taron Mauludi a Katsina, Sun Halaka Mutum 20 Da Sace Wasu Da Dama

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki ana tsaka da gudanar da bikin Mauludi a ƙauyen Kusa na jihar Katsina
  • Ƴan bindigan waɗanda suka buɗewa mutanen da ke wurin wuta, sun halaka mutane masu yawa tare da raunata wasu
  • Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar harin inda ta ce tana cigaba da gudanar da bincike domin cafke maharan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun halaka mutane da dama da suka haɗa da mata da ƙananan yara a lokacin da suka kai hari wurin wani taron bikin Mauludi a ƙauyen Kusa da ke ƙaramar hukumar Musawa a jihar Katsina.

Sai dai, akwai alƙaluman da ke karo da juna na adadin waɗanda suka mutu, inda wasu suka ce aƙalla gawarwaki 20 ne aka ɗauko daga wurin da lamarin ya faru yayin da wasu suka ce adadin ya kai 14, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane a wurin Maulidi, 'yan bindiga sun ƙara kai ƙazamin hari a jihar Katsina

'Yan bindiga sun halaka masu Mauludi a Katsina
'Yan bindiga sun halaka masu bikin Mauludi a jihar Katsina Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu mutum aƙalla 17 sun samu raunuka, inda aka kwantar da wasu daga cikinsu a asibitin 'Orthopedic' na Katsina domin ciro harsashi, yayin da wasu ke kwance a babban asibitin Musawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya auku

A cewar wani mazaunin garin, ƴan bindigan sun buɗe wuta kan mutanen ne da misalin ƙarfe 11:05 na daren ranar Lahadi, inda kuma suka yi awon gaba da mutane da dama daga wurin.

"Ƴan bindigan sun kewaye wurin da ake gudanar da Mauludin sannan suka harbi mahalarta taron, inda suka jikkata mutane da dama tare da yin awon gaba da wasu." A cewarsa.

Ya ƙara da cewa kafin isowar jami’an tsaro maharan sun arce zuwa maɓoyarsu.

Menene abin da ƴan sanda suka ce kan harin?

Da yake tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce ƴan bindigar sun kai hari inda suka harbe mutum 18 tare da raunata su, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar Zamfara, sun yi awon gaba da mutum 5

"An kwashe su zuwa asibiti domin yi musu magani. Daga baya, biyu daga cikinsu sun rasu. Ana cigaba da gudanar da bincike domin cafkewa tare da gurfanar da waɗanda suka kai harin." A cewarsa.

Ƴan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mutane

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a garin Maru hedikwatar ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka halaka mutum ɗaya.

Miyagun ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum biyar tare da ƙona wara motar sintiri ta ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng