Babban Sarkin Yarbawa Ya Bayyana Ma’anar Tambarin da Aka Saba Gani a Hular Tinubu
- Duk wanda yasan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, to ya san shi da hularsa mai dauke da wani irin tambari, kamar lamba 8 a kwance
- Tun daga zamanin da yake gwamnan jihar Legas, an ga dan siyasar sanye da huluna daban-daban amma masu dauke da wannan tambari
- Haka zalika, da yawa daga cikin magoya bayan Shugaba Tinubu na sanya wannan hula; yanzu kuma Sarkin Iwoland, Oba Akanbi ya bayyana ma'anar wannan tambari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iwo, Jihar Osun - Oba Abdulrosheed Akanbi, Sarkin Iwoland, ya ce ma'anar wannan tambari da ke jikin hular Shugaban Kasa Bola Tinubu ita ce "alamar kaca".
Oba Akanbi ya ce "ya gamsu" da Shugaba Tinubu da kuma kasancewarsa shugaban kasar Najeriya a yanzu.
Duk da cewa ya kasance tsohon gwamnan jihar Lagos, amma Shugaba Tinubu na da tsatso a kabilar Iragbiji da ke jihar Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akanbi, wanda basarake ne a Osun, ya nuna yakininsa na cewar Najeriya karkashin Shugaba Tinubu, "za ta zama abin alfaharin kowa".
Oba Akanbi ya wallafa hakan a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba, inda ya ke cewa:
"Mutumina na kaina wanda nake alfahari da shi. Ya jima yana dakon abin tunkahonsa na 'gicciye' dauke da 'alamar sarka' a jikin hularsa.
"Wannan 'yanci ne gare mu. Najeriya za ta sake zama abin alfahari."
Hular Tinubu mai dauke da tambarin ban mamaki ta tayar da hazo a intanet
A cikin wani labarin makamancin wannan, jaridar Legit Hausa ta ruwaito yadda Tinubu ya zama abin koyi ga wasu 'yan Najeriya wadanda ke dakon sayen hularsa mai dauke da tambarin sarka, wacce za a sayar a shafin sada zumunta na X.
A cikin wata wallafa da Legit ta ci karo da ita, wani ma'abocin shafin mai suna @Jbmomoh, ya sanar da mabiyansa cewa akwai hulunan da ya ke son sayar wa. Hulunan iri daya ne sak da wadanda Tinubu ke saka wa.
Aisha ta zana tambarin hular Tinubu a hannunta
Haka zalika jaridar Legit Hausa ta kuma ruwaito yadda Aisha Buhari ta zana hoton tambarin hular Tinubu a hannunta.
A cikin wani bidiyo da kungiyar Jide Sanwo-Olu, @JideSGroup ta wallafa a shafinta na X, an ga Aisha ta zanen tambarin hular Tinubu a hannunta, yayin da take murmushi tare da daga hannun ga jama'a.
Munatane sun tofa albarkacin bakinsu kan sabuwar hular Tinubu
A wani labarin makamancin wannan, Legit ta ruwaito cewa an hango Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa yana zagayawa tare da jami'an tsaron sa. Haka zalika anga shugaban kasar sanye da sabuwar hula mai dauke da tambarinsa.
Bidiyon ya bayyana ne awanni 24 bayan da shugaban kasar ya yi zama na biyu da majalisar zartaswar gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng