Hare-Haren Sojojin Sama Sun Halaka Ƴan Ta'adda Masu Yawa a Yankuna 2 Na Arewacin Najeriya
- Dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda masu anwasu hare-hare da suka kai
- A yankin Arewa maso Gabas, dakarun sojojin sun farmaki maɓoyar ƴan ta'addan Boko Haram inda suka halaka da yawa daga cikinsu
- A yankin Arewa maso Yamma, dakarun sojojin sun farmaki maɓoyar wasu manyan shugabannin ƴan ta'adda inda suka halaka masu yawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Dakarun sojojin sama na atisayen 'Operation Hadin Kai' (OPHK) a Arewa maso Gabas da na atisayen 'Operation Hadarin Daji' (OPHD) a Arewa maso Yamma sun kashe yan ta'adda da dama a wasu hare-hare.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da darektan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya fitar ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba a Abuja.
Gabkwet ya ce an kai hare-haren ne tare sa haɗin gwiwar dakarun sojojin ƙasa tare da sauran jami'an tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yankin Arewa maso Gabas, Gabkwet ya ce, hare-haren da rundunar sojojin sama ta OPHK ta kai a ranar 3 ga watan Nuwamba, ya kai ga kakkaɓe ƴan ta’adda da dama a wurin taronsu da ke kusa da Degbawa, cikin tsaunin Mandara a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
A yankin Arewa maso Yamma, Gabkwet ya ce, rundunar sojojin sama ta OPHD a ranar 1 ga watan Nuwamba, ta kai wasu jerin hare-hare ta sama a ƙaramar hukumar Kankara da ke jihar Katsina, inda suka farmaki maɓoyar wani fitaccen ɗan ta'addan mai suna Babaru.
Dakarun sojojin sama sun farmaki maɓoyar ƴan ta'adda
A cewarsa, Babaru yana da hannu a cikin ayyukan ta'addanci da dama a faɗin Kankara da kuma ƙananan hukumomin da ke makwabtaka da ita a jihar Katsina.
A cewarsa, harin da aka kai ta sama ya lalata maboyar Babaru tare da halaka ƴan ta’adda da dama, duk da cewa babu tabbacin cewa Babaru na cikin waɗanda aka kashe.
Gabkwet ya ce an kuma kai hare-hare ta sama a maɓoyar wani shugaban ƴan ta'adda da ake kira Mai Solar da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
A cewarsa, hare-haren da aka kai ta sama sun yi nasarar lalata maɓoyar da shugaban ƴan ta'addan da yaransa ke amfani da ita.
"An samu nasarar kai harin yayin da aka lura da wasu tsirarun ƴan ta'adda da suka tsira na guduwa daga wajen. Babu tabbacin ko Mai Solar na cikin ƴan ta'addan da aka halaka." A cewarsa.
Dakarun Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta'adda
A wani labarin kuma, dakarun sojojin Najeriya sun salwantar da rayukan ƴan ta'adda masu yawa a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'addan ne yayin da suka daƙile wani hari da suka kai a ƙauyen Karazau cikin ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar.
Asali: Legit.ng