Babban Malamin Addinin Musulunci Sheikh Yusuf Ali Ya Rasu a Kano
- An yi rashin babban malamin addinin musuluncin nan Sheikh Yusuf Ali (Sarkin malamai Gaya) wanda ya rasu ranar Lahadi a birnin Kano
- Babban malamin addinin musuluncin wanda ya rasu yana da shekara 73 a duniya, ya yi aiki a fannin shari'a lokacin da yake raye
- Za a gudanar da jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidansa da ke cikin ƙwaryar birnin Kano a ranar Litinin, 5 ga watan Nuwamba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Kano - Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Kano Sheikh Yusuf Ali ya rasu.
Sheikh Yusuf Ali (Sarkin malaman Gaya) ya rasu yana da shekara 73 a duniya.
Ɗan siyasar nan kuma ɗa a wajen malamin, Muslihu Yusuf Ali, shi ne ya sanar da rasuwarsa ta shafinsa na Facebook a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene Sheikh Yusuf Ali?
An haife shi a shekara ta 1950 a garin Gaya da ke jihar Kano, marigayin malamin addinin Musuluncin ya fara aikinsa a fannin shari'a a shekarar 1974 a kotun shari'ar musulunci a matsayin magatakarda, cewar rahoton Daily Nigerian.
Daga nan marigayin ya zama babban magatakarda, mataimakin rajistara, rajistara, alƙalin kotun babbar kotun shari'ar musulunci da darekta a babbar kotun shari'ar musulunci.
Ya yi ritaya a shekarar 2009 kuma ya cigaba da koyar da addinin Musulunci.
Za a yi jana'izarsa a gidansa da ke Unguwar Tudun Maliki cikin ƙwaryar birnin Kano da ƙarfe 1:30 na rana a yau Litinin, 6 ga watan Nuwamba.
Sheikh Ibrahim H. Musa ya riga mu gidan gaskiya
A wani rahoton, Sheikh Ibrahim H. Musa wanda aka fi da Albanin Kuri ya riga mu gidan gaskiya a gidansa da ke birnin Gombe na jihar Gombe.
Malamin addinin musuluncin ya rasu ne bayan wasu ƴan ta'adda sun farmake shi tare da halaka shi a cikin gidansa.
Alƙalin Babbar Kotun Kwara Ya Rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa alƙalin babbar kotun jihar Kwara, Sikiru Adeyinka Oyinloye, ya rasu yana da shekara 58 a duniya.
Marigayi Alƙalin ya rasu ne ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, 2023 bayan kwashe dogon lokaci yana fama da ciwon da ya shafi wuyansa.
Asali: Legit.ng