Jerin Sanatocin da Kotun Daukaka Kara Ta Kora Daga Kujerun Majalisar Dokokin Kasa

Jerin Sanatocin da Kotun Daukaka Kara Ta Kora Daga Kujerun Majalisar Dokokin Kasa

Sannu a hankali fagen siyasar Najeriya na samun sauyi, inda ‘yan jam’iyyun adawa ke samun galaba tare da kalubalantar jam’iyyu masu ci, musamman jam’iyyar APC.

Ana yiwa zaben 2023 ganin daya daga cikin zabuka mafi nagarta a tarihin Najeriya, inda jam'iyyar Labour ta yi kamari da suna a lokacin zaben.

Bayan sakamakon zaben bana, ‘yan takara a dukkan matakai da suka hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da na jam’iyyar Labour, suka kalubalanci rashin nasarar da Bola Ahmad Tinubu.

Wannan fafatawa ta shari’a bata bar ‘yan takarar Sanata daga manyan jam’iyyun siyasa ba a zaben da suka hada da PDP da APC da kuma Labour ba.

Wadanda aka kora daga majalisa
Sanatocin da aka kora daga majalisa | Hoto: Elisha Abbo, Darlington Nwokocha
Asali: Twitter

A wani yanayi na daban, kotun daukaka kara ta kori Sanatoci daga wadannan manyan jam’iyyun siyasa cikin mako guda kacal bayan ta fara zamanta a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar a runtuma kame, 'yan kauye sun yi wa alkali jina-jina a jihar Gombe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin sunayen sanatocin da aka kora zuwa yanzu da jam’iyyunsu na siyasa:

Elisha Abbo (APC)

Sanatan mai wakiltar Adamawa ta Arewa shi ne dan majalisar dattawa na farko da kotun daukaka kara ta kora. Ya zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kitsa komai da kuma yin tasiri a kotu a kansa.

Sai dai kotun ta kori Abbo ne bayan ta cire adadin kuri’un bogi a rumfunan zabe tare da bayyana abokin hamayyarsa Amos Yohanna na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Adamawa ta Arewa.

Bayan kwanaki biyu shugaban majalisar dattawa Akpabio ya rantsar da Yohanna a matsayin Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa.

Abubakar Sadiku Ohere (APC)

Sadiku-Ohere mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, shi ne dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC da kotun daukaka kara ta kora bayan doguwar zaman shari’a da abokiyar hamayyarsa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta PDP.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta rusa zaben sanatan LP, ta bayyana sahihin wanda ya lashe zabe

Tun da farko kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ke zamanta a Lokoja ta kori tsohon Sanatan na APC amma Sadiku-Ohere ya nemi a yi masa hukunci a kotun daukaka kara.

Tuni dai an rantsar da Akpoti-Uduaghan a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ta 10.

Simon Mwadkwon (PDP)

Mwadkwon ne dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Filato ta Arewa ta Tsakiya da kotun daukaka kara ta kora yayin da kotun ta bayar da umarnin sake zaben majalisar dattawa cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Sai dai Mwadkwon wanda shi ne shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin kasa ta 10, ya bayyana kwarin gwiwar komawa majalisar dattawa nan da kwanaki 90 masu zuwa kamar yadda kotun daukaka kara a jihar ta bayyana.

Korarren sanatan ya bayyana kwarin gwiwarsa ne a lokacin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar PDP a jihar kwanaki bayan da kotun daukaka kara ta kore shi.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan makomar zaben sabon sanatan APC

Darlington Nwokocha (Jam’iyyar Labour)

Nwokocha, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Abia ta Tsakiya shi ma kotun daukaka kara ta aike dashi wajen majalisa bayan da ya fafata da abokin hamayyarsa a jam’iyyar PDP, Augustine Akobundu.

Sanatan da aka kora daga jam’iyyar ta Labour shi ne babban mai tsawatarwa a majalisar dattijai ta 10.

Daga bisani kotun daukaka kara ta bayyana Akobundu a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Akobundu dai tsohon kanal din soja mai ritaya ne kuma tsohon karamin ministan tsaro. Ya kuma taba zama sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.