Tashin Hankali Yayin da Walkiya Ta Kashe Dalibai Suna Tsaka da Buga Kwalla a Anambra

Tashin Hankali Yayin da Walkiya Ta Kashe Dalibai Suna Tsaka da Buga Kwalla a Anambra

  • An yi tsawar da ta zo da walkiya, ta hallaka wasu dalibai da ke makarantar sakandare a jihar Anambra
  • An kuma bayyana cewa, akalla wasu shida ne suka jikkata, yanzu haka suna samun kulawar asibiti
  • Ba wannan ne karon farko da ake yin tsawar da ke kai wa ga mutuwar mutane da yawa ba a Najeriya

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Anambra - Walkiya ta kashe dalibai uku na makarantar babbar sakandare (SS3) a karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) cewa, walkiyar ta rufta da dalibai maza tara ne da ke buga wasan kwallon kafa da takwarorinsu a filin makarantar.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar a runtuma kame, 'yan kauye sun yi wa alkali jina-jina a jihar Gombe

Lokacin da lamarin ya faru, an ce daliban na motsa jiki ne a daidai lokacin da hadari ya taso, inda suke kokarin fara wasa.

Tsawa ta kashe daliban sakandare
Tsawa ta kashe dalibai a Anambra | Hoto: PM News
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da ake ciki a asibiti

A cewar wani malami, an tattara daliban zuwa asibiti, inda uku uka rasu shida kuwa ke ci gaba da karbar kulawar likitoci.

Wata mazauniyar yankin mai suna Misis Hope Egwu, ta shaida cewa, labarin iftila’in ya bazu ne a ranar Lahadi, PM News ta ruwaito.

A asibitin na Awka, iyaye da masu jajantawa sun kutsa kai cikin dakin da aka ajiye wadanda suka tsira, inda suke samun kulawa.

Wani likitan da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida ya ce an kawo uku daga cikin yara a mace, amma shida suna raye a halin da ake ciki.

Abin da 'yan sanda ke cewa

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno, mata ta auri mijin da ba ya haihuwa cikin rashin sani, zamansu ya yi tsami

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce ba a kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda ba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, Farfesa Chukwudi Okani, kwararren likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, Awka, ya ce bala’i ne da ya sha faruwa.

Ya shawarci jama’a su sanya na’urorin da ke kama tsawa a gine-ginensu domin kakkabe igiyar da ke tafe da ruwa da walkiya.

Hakan ta faru a wani wuri

A wani labarin, tsawar kwarankwatsa, hasken walkiya, da ambaliyar ruwan sama lokacin damina sun dade suna haifar da asarar rayuka da dukiyoyi lokacin damuna.

Irin wadannan matsaloli sun fi tsanani a kasashen da ke yankin nahiyar Afrika ta gabas.

'Yan sanda a gabashin kasar Uganda sun sanar da cewa hasken walkiya ya hallaka yara goma yayin da suke wasan kwallo ana ruwan sama

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.