Damina: Hasken walkiya ya kashe yara 10 yayin wasan kwallo

Damina: Hasken walkiya ya kashe yara 10 yayin wasan kwallo

- Tsawar kwarankwatsa, hasken walkiya, da ambaliyar ruwan sama lokacin damina sun dade suna haifar da asarar rayuka da dukiyoyi lokacin damuna

- Irin wadannan matsaloli sun fi tsanani a kasashen da ke yankin nahiyar Afrika ta gabas

- 'Yan sanda a gabashin kasar Uganda sun sanar da cewa hasken walkiya ya hallaka yara goma yayin da suke wasan kwallo ana ruwan sama

Rundunar 'yan sanda a gabashin kasar Uganda ta sanar da cewa hasken walkiya ya hallaka yara goma yayin da jama'a ke fakewa bayan an saki wata babbar tsawa sakamakon barkewar ruwan sama a lokacin da suke wasan kwallon kafa.

Josephine Angucia, kakakin rundunar 'yan sanda a birnin Arua da ke Arewa maso yamma da babban birnin Kamfala ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na dpa cewa yaran; wadanda shekarunsu basu wuce 11 zuwa 16 ba, sun mutu yayin da suka fake a wani kango.

"Kananan yara ne da ke fitowa su buga wasan kwallon kafa duk lokacin da ruwan sama ya sauko, sune hasken walkiya ya hallaka," a cewar Angucia.

Yaran sun fake ne a cikin wani kango mai ciyawa a lokacin da hasken walkiyar ya sauka a kansu da yammacin ranar Alhamis.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa' "wasan kwallon kafa suke bugawa a fili ma fi kusa, wasu yaran guda hudu sun samu raunuka.

"Tun jiya dangi da 'yan uwa suka fara ziyartar dakin ajiyar gawa domin daukar gawar 'ya'yansu, tuni yanzu haka wasu iyayen sun fara binne gawar 'ya'yansu," kamar yadda Agucia ta kara bayyanawa.

Damina: Hasken walkiya ya kashe yara 10 yayin wasan kwallo
Hasken walkiya
Asali: Twitter

Angrucia ta kara da cewa; "irin wannan walkiya mai hatsari ba bakon abu bane a kasashen gabashin nahiyar Afrika, iyaye su tashi tsaye wajen hana yaransu wasa yayin da ruwan sama ke zuba."

DUBA WANNAN: Kwamishina, Hajiya Aisha, ta yi murabus kan zargin karkatar da N300m

"A mafi yawancin lokuta filayen wasa suna kusa da makarantu, mu na shawartar makarantu su fara amfani da na'urorin da ke dauke da fasahar kashe kaifin walkiya domin kiyaye rayuwar yara."

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne hukumar kula da yanayi a kasar Uganda ta yi gargadin cewa za a samu karuwar saukar ruwan sama a daminar bana.

Walkiya, tsawar kwarankwatsa, da ambaliyar ruwan sama sun dade suna haddasa asarar rayuka da kadarori a sassan kasar Uganda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel