Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya hallaka mutane 183, mutane 215 sun jikkata

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya hallaka mutane 183, mutane 215 sun jikkata

Akalla mutane dari da tamanin da uku ne suka rigamu gidan gaskiya a sandiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe tsawon lokaci ana yi a kasar Ruwanda, inji rahoton Kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da mutanen da suka mutu, sama da mutane dari biyu da goma sha biyar ne suka samu rauni daban daban, kamar yadda Ministan kula da bala’o’I da yan gudun Hijira na kasar Ruwanda ya tabbatar.

KU KARANTA: Buhari ya kulla wata cinikayya da gwamnatin Kasar China da zata rugurguza darajan Dalan Amurka

Ministan ya bayyana rashen rashen da aka yi da kuma raunin da mutanen suka samu ya faru ne a watanni hudu kacal, inda ya kara da cewa ruwan saman da aka sha yayi sanadin walkiya, tsawa da kuma ambaliya da suka lalata gidaje sama da 9,974.

Bugu da kari kimanin kadada 2,450 na gonakai ne ruwan barnata, da kuma makarantu 21 da yayi awon gaba dasu, kamar yadda alkalumman suka bayyana.

A ranar Laraba 2 ga watan Afrilu ne Gwamnatin kasar Ruwanda ta bayyana alhininta tare da jajanta ma jama’an kasar, musamman wadanda suka rasa yan uwansu da wadanda bala’in ya shafa.

Hakazalika gwamnatin kasar ta tattauna hanyoyin tallafa ma wadanda abin ya shafa, tare da samar da dabarun gyara barnar da ruwan yayi, da kuma kare aukuwar hakan a gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng