So Gamon Jini: Daga Yanke Mata Farce, Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Soyayya da Mai Yankan Kumba
- Wata mata ‘yar Najeriya ta girgiza al’ummar kafar sada zumunta yayin da ta nuna bidiyon wani mai yankan farce
- Budurwar ta yi masa bidiyo ne taya murmurshi a lokacin da ya yanke mata farce, inda tace ita fa tana kaunarsa
- Yayin da wasu ke bayyana ra’ayin ya kamata ta biya shi kudinsa, wasu sun ce yaba masa bisa kwarewa a aikinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Wata budurwa ‘yar Najeriya ta girgiza intanet, ta bayyana kaunarta ga wani matashi mai sana’ar yankan farce.
A wani bidiyon da aka gana a Tiktok, budurwar ta nuna lokacin da matashin ke yi mata yankan farce cikin kwarewa.
Matashin ya yi murmushi kana ya yi mata wani kallo. Budurwar mai suna @Niffynelly sai ta dauko wayarta tare da daukar bidiyon selfie tare da matashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ki biya shi kudansa
Mutane da dama a kafar sada zumunta sun yi dariya, inda suka bayyana bukatar ta biya shi kudinsa kawai, ban da wayau.
Wasu sun yabawa matashin bisa aiki da kwarewa, wasu kuwa suka bayyana cewa kyakkyawan matashi ne
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a a kafar sada zumunta
@AbdulBasit67:
"Dole dai ki biya shi bayan nan sai ki nemi ya yanke miki a kyauta.”
kassimabdullai:
"Ina taya ki murna ‘yar uwa kada ki damu da abin da mutane za su ce kawai ki bi zuciyarki.”
Ejeagu Justus:
"Wannan dai yaro ne don Allah kada ki bata shi.”
evil 4kt:
'Wannan kyakkyawan yaro ne kuma da gani idan ya samu rayuwa mai kyau zai ma fi haka kyau, ina maku addu’a.”
Tobeelorbah:
"Abin dariya yanzu wani ya yanke min farce ko kallo na ma bai yi.”
Black beauty:
"Matashi na kallonki kina dariya kawai ki biya shi kudinsa cif-cif.”
Kudin da mai yankan farce ke samu
A bangare guda, an yi fira da mai yankan farce, ya fadi irin kudaden da suke samu a wannan sana'ar da wasu suka raina.
A cewar Ibrahim Kabiru, yakan samu kudin da basu yi kasa da N45,000 duk wata a sana'ar da yake yi a jihar Edo.
Sana'ar yankan farce dai sana'a ce da ake samun almajirai ke yi a Arewacin Najeriya, galibi Hausawa ke yinta.
Asali: Legit.ng