“Na Sha Kuka”: Yar Najeriya Ta Yada Hirar da Ta Gani a Wayar Mijinta
- Wata yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya kan hirar WhatsApp da ta gano a wayar mijinta
- Matar wacce ta karaya ta koka cewa yanzu tana ji kamar ita kawai ke auren kanta
- Koken matar ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da mutane suka shawarceta game da matsalar da take fuskanta a aurenta
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata yar Najeriya ta duba wayar mijinta sannan ta karaya da sakon da ya aikewa daya daga cikin abokan aikinsa a WhatsApp.
Matar auren da ba a bayyana sunanta ba ta yada sakon a dandalin Facebook, yayin da take neman shawara kan abun yi.
A cewarta, sun samu sabani da shi yan makonni da suka wuce kuma ta yi tsammanin za su yi sulhu a tsakaninsu amma sai mijin ya bata kunya ta hanyar sako yan uwansa a ciki tare da fada masu sirrinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce abun ya sa ta kuka sosai. Kalamanta:
"Na duba wayar mijina sannan na ga sakon da ya aikawa abokin aikinsa.
"Yan makonni da suka gabata ni da mijina mun samu sabani, ya kamata mu yi sulhu tsakaninmu amma mijina ya kira yan uwansa kai na sannan ya fada masu dukka sirrinmu a gidan, na yi kuka sosai saboda bana so mutum na uku ya tsoma baki a harkar aurenmu."
Ta ce mijinta ya ba ta hakuri cikin hawaye kwatsam sai ya canja dabi'unsa a kanta bayan nan.
"Mijina ya gane cewa abun ya yi mun ciwo sosai, sannan ya fara bani hakuri har kuka ya yi yana rokona da tsakar dare, sannan na fada mashi cewa na yafe masa.
"Amma sai jiya, mijina ya fara janyewa daga gareni, yana daukar matakai ba tare da sanar dani ba, wanda ba haka ya saba ba a baya.
"Ya turawa mahaifinsa kudi ba tare da ya fada mani ba, kuma yanzu na ga wannan sakon a wayarsa."
Matar wacce ke cike da radadi ta ce yanzu bata jin ta tsira.
"Bana jin na tsira a auren nan yanzu, muna da yara 2 kuma ina aiki.
"Abun ya yi kamar ina auren kaina ne.
"Ku bani shawara."
Jama'a sun yi martani kan lamarin
Isoken Igbinosun ta ce:
"Haka aure yake? Kawai kuna tsoratamu mu da bamu yi aure ba. Allah zai kawo sauki."
Mercy Salawu ta ce:
"Babu wani abun bayar da shawara fa. Sakon a bayyane yake kamar fuskar wannan wayar fa. Auren ya dade da wargajewa tun da dadewa."
Omolara Omowumi Elegbede ta ce:
"Allah ya kyauta sai ya fada maki kafin ya ba mahaifinsa da mahaifiyarsa kudi? Aure baya nufin ke ce kike da shi gaba daya. Don Allah ki kwantar da hankalinki Hajiya."
Bidiyon shagalin bikin amarya da hoton ango
A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a sun yi cece-kuce a kan bidiyon shagalin bikin da aka yi tsakanin wani ango da baya nan da amaryarsa yar Najeriya.
Wani mai amfani da dandalin X mai suna @Folasheycrown22, ya yada bidiyon kan dandalin dauke da tambaya.
Asali: Legit.ng