"Kwanakin Ƴan Ta'adda Sun Kusa Ƙarewa" Sojoji Sun Halaka Sama da 60, Sun Kama 190 a Jihohin Arewa

"Kwanakin Ƴan Ta'adda Sun Kusa Ƙarewa" Sojoji Sun Halaka Sama da 60, Sun Kama 190 a Jihohin Arewa

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ragowar kwanakin da suka rage wa ƴan ta'adda a duniya ba su da yawa kuma a kididdige suke
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce sojoji sun tura yan bindiga 67 barzahu sun kama 170 a makon jiya kaɗai
  • A cewarsa yaƙin yanzu aka fara, matuƙar masu tada kayar baya ba su saduda sun miƙa wuya ba, sojoji zasu tura su inda ba a dawowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta gargadi ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da cewa kwanakin da ya rage musu kididdigaggu ne yayin da sojoji suka samu nasarori a mako ɗaya.

Kara karanta wannan

Tukur Buratai ya fasa kwai kan ainihin wadanda suka kawo rashin tsaro a Najeriya

Sojoji sun ragargaji yan ta'adda a shiyyoyin arewa.
DHQ: Kwanakin da Suka Rage Wa Yan Bindiga da Yan Ta'adda Kididdigaggu Ne Hoto: NigerianArmy
Asali: Facebook

Mai magana da yawun hedkwatar tsaron (DHQ) na ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a a Abuja.

Daily Trust ta rahoto kakakin DHQ na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sojoji za su ci gaba da hana ‘yan ta’adda, masu tayar da kayar baya da masu tsattsauran ra’ayi damar cimma burinsu na son rai da rashin imani."
"Yaƙi yanzu aka fara kuma ragowar kwanakinsu ba su da yawa a doron duniya matuƙar ba su miƙa wuya sun tuba ba."

Nasarorin da sojoji suka samu a mako ɗaya

Da yake bayani kan nasarorin da sojoji suka samu a maƙo ɗaya kaɗai, Buba ya ce dakaru sun sheƙe yan ta'adda 67, sun kama 190 yayin da suka ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su.

Ya ce dakarun sojoji sun samu wannan nasara ne a samamen da suka kai daban-daban a shiyyoyin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

A cewarsa, jami'an sojin sun kuma jikkata ƴan bindiga da ƴan ta'adda da yawa, sun lalata sansanoninsu da ɓata masu kayan aiki masu yawa cikin mako ɗaya.

Buba ya ce sojoji sun kwato makamai iri-iri guda 112 da alburusai kala daban daban 989 a shiyyoyin da suka kai samame kan ƴan ta'adda, The Nation ta ruwaito.

Ya kara da cewa sun samu nasarar kwato motoci 23, babura 33, wayoyin hannu 31, na rediyon baofeng, keke, kwalabe, gatari, kyamarar dijital da kudi naira miliyan 3.2.

Jirgin sama ya samu tangarɗa yayin sauka a Ibadan

Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin sama mai zaman kansa ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman Ibadan da ke Alakia a jihar Oyo.

Jirgin saman wanda ya ɗauko fasinjoji ciki har da Ministan Bola Tinubu, ya kauce wa hanya, ya yi cikin ciyayi sa'ilin sauka a filin jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262