Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5, Sun Jikkata 4 Yayin da Suka Kai Farmaki a Jihar Sokoto

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 5, Sun Jikkata 4 Yayin da Suka Kai Farmaki a Jihar Sokoto

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari garin Duhuwa, a karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki al'ummar gari inda suka kashe mutum biyar tare da raunata wasu hudu
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al'amarin a ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, inda ta ce an yi garkuwa da wasu da dama

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewar tsagerun yan bindiga sun farmaki garin Duhuwa, da ke karamar hukumar Wurno ta jihar, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata wasu hudu.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya ce an kuma sace wasu da dama a yayin harin, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan makomar zaben sabon sanatan APC

Yan bindiga sun halaka mutum biyar a Sokoto
Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyar, Sun Jikkata Hudu Yayin da Suka Kai Farmaki a Jihar Sokoto Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Mutum shida aka kashe ba hudu ba, mazaunin garin Duhuwa

Sai dai kuma, wani mazaunin kauyen mai suna Dalhatu Duhuwa, wanda ya zanta da jaridar Punch, ya bayyana cewa mutum shida aka kashe ba biyar ba kamar yadda rundunar yan sandar ta sanar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tabbatar da adadin wadanda suka mutu, Duhuwa ya ce lamarin ya fara ne tun da misalin karfe 10:30 na daren ranar Alhamis har zuwa misalin karfe 12:10 na tsakar dare lokacin da yan bindigar suka bar kauyen.

Mazaunin kauyen ya ce:

"Lamarin ya fara da misalin 10:30 na dare sannan ya kai 12:10 na tsakar dare lokacin da yan bindigar suka wuce bayan sun kashe akalla mutum shida, dukkansu maza, suka raunata mutum hudu sannan suka sace wasu mata.
"Koda dai yan sanda da jami'an sauran hukumomin tsaro sun zo da misalin 12:25 na tsakar dare, sun samu labarin ne ta wajen wasunmu da suka kasance masu ruwa da tsaki a soshiyal midiya ta hanyar wallafarmu.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar tsohon gwamnan Gombe

"Sun yi kokarin bin yan bindigar har cikin jeji amma abun takaici basu gan su ba domin sun dade da yin nisa."

Ina yan bindigar suke a yanzu?

A halin da ake ciki, Duhuwa wanda ya kasance mai fada aji a soshiyal midiya, ya roki jami'an tsaron da ke kauyen a yanzu haka a kan su tsawaita zamansu sannan su zamo masu lura sosai.

Ya ce akwai bayanai da ke yawo cewa yan bindigar sun boye a jejin da ke kusa da kauyen kuma suna iya sake kai hari.

Radda ya bayyana barnar yan bindiga a Katsina

A wani labarin, mun ji cewa akalla makarantu 123 ne aka ce an rufe su gaba daya a jihar Katsina sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun da ke addabar al’ummar jihar.

Haka nan kuma gwamnatin jihar ta bayyana cewa akalla cibiyoyin kiwon lafiya 58 ne suka daina aiki kwata-kwata sakamakon matsalar rashin tsaro, Channels TV ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng