Badakalar kudin Abacha: Najeriya ta samu zambar kudi dala miliyan 311 daga kasashen waje
Daga karshe, gwamnatin kasar Amurka da kasar Bailiwick of Jersey sun aiko ma Najeriya dala miliyan 311 daga cikin kudaden da tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya taskance a can.
Daily Nigerian ta ruwaito Ministan sharia, Abubakar Malami ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin ta bakin mai magana da yawunsa Dakta Umar Gwandu.
KU KARANTA: Ji ka karu: Matakai 6 da ake bukata a dauka ga wanda ya yi mu’amala da mai cutar COVID19
Malami ya bayyana cewa kasashen biyu sun aiko ma Najeriya $311,797,866.11, wanda ya haura kudin da suka yi alkawarin aikowa tun a watan Feburairun 2020, watau $308m.
Sanarwar ta ce kudaden sun karu daga $308m zuwa $311m ne sakamakon kudin ruwa da suka karu a kan kudin daga watan Feburairu zuwa watan Afrilun da kudin suka shiga hannun CBN.
Ministan yace a shekarar 2014 aka fara shari’ar dawo da kudaden Najeriya, yayin da tattaunawar diflomasiyya tsakanin game da dawo da kudin kuma sun fara ne a shekarar 2018.
“Wannan yarjejeniya da aka yi an gina ta ne a kan dokokin kasa da kasa da hadin kan kasa da kasa na dawo da kudin da kuma lura da kashe su. Hakan kari ne ga dala miliyan 322 da gwamnatin Buhari ta amso daga kasar Switzerland a shekarar 2018.
“Wanda a yanz haka ake kashe su wajen tallafa ma talakawa gajiyayyu kamar yadda aka cimma yarjejeniya tsakanin kasashen biyu da kuma bankin duniya.” Inji shi.
Minista Malami, wanda ya jagoranci tawagar Najeriya a tattaunawar ya bayyana an kafa tarihi da wannan tsarin dawo da kudaden a duniya, saboda za’a saka ma wadanda rashawa ya cutar.
“Kamar yadda aka yi yarjejeniya a 2020, an tura ma babban bankin Najeriya kudin, kuma za’a mika su ga hukumar kula da asusu mai zaman kanta, NSIA, nan da kwanaki 14, saboda NSIA ne zasu gudanar da ayyukan da aka shirya yi da kudaden.
“Ayyukan da za’a gudanar da kudin sun hada da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, Abuja – Kano, da kuma gadar Neja ta biyu, a yanzu haka gwamnati na kan kafa kwamitin kula da ayyukan.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng