Matasa Yan Bautar Ƙasa NYSC Sun Kuɓuta Daga Hannun Yan Bindiga, Sojoji da Yan Sanda Sun Yi Kokari
- Dakarun soji da taimakon 'yan sanda sun samu nasarar ceto 'yan bautar ƙasa biyu daga hannun ƴan bindiga a jihar Katsina
- Kakakin hukumar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce ƴan bindiga sun sace mambobin NYSC ne a hanyar zuwa Katsina daga Edo
- Ya ce yanzu haka an kai su asibiti domin bincikar lafiyarsu kuma suna hannun ƴan sanda a Kankara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Katsina - Dakarun rundunar sojin Najeriya da haɗin guiwar jami'an ƴan sanda sun ceto ƴan bautar ƙasa NYSC biyu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Katsina.
Channels tv ta ruwaito cewa ƴan bindiga sun sace ƴan bautar ƙasar ne a ƙauyen Yargoje da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Kastina.
Jami'an tsaron sun samu nasarar ceto matasan ƴan bautar ƙasar guda 2 ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, 2023.
Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasan Najeriya, Onyema Nwachukwu, ne ya tabbatar da wannan nasara a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka ceto mambobin NYSC
Ya ce ƴan bindiga sun yi garkuwa da mambobin NYSC ne yayin da suke hanyar zuwa wurin da aka tura su a Katsina daga jihar Edo.
A rahoton The Cable, Nwachukwu ya ce:
"A wani samamen haɗin guiwa ranar Alhamis, dakarun sojin Birged na 17 tare da haɗin guiwar jami'an yan sanda sun ceto ƴan bautar ƙasa 2 da aka sace a Yargoje, ƙaramar hukumar Kanƙara a Katsina."
"Namijin kokari da jajircewar jami'an tsaro ne ya sa mambobin NYSC suka kubuta kuma suka dawo cikin ƙoshin lafiya. Ƴan bindiga sun sace su a hanyar zuwa Katsina daga Edo."
"Gaggawar kai ɗaukin da sojoji tare da ƴan sanda suka yi ne ya yi sanadin kubutar mambobin NYSC guda biyu mata daga hannu masu garkuwa."
'Yan bindiga sun yi garkuwa da CoS na shugaban majalisar dokokin Adamawa, sun turo saƙo mai tada hankali
Ya ƙara da cewa tuni aka kai waɗanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsu kuma yanzu haka suna hannun ƴan sandan Ƙanƙara.
Kakakin rundunar sojin ya bukaci jama’a da su bada hadin kai tare da tallafa wa sojoji da bayanan sirri a kokarinsu na kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.
An kashe miji a kokarin kare matarsa
A kokarin kare mutuncin matarsa, wani magidanci ɗan shekara 25, Ibrahim Ahmadu ya rasa rayuwarsa a jihar Bauchi.
Hukumar ƴan sanda ta bayyana cewa wasu ƴan daba suka tare ma'auratan, suka nemi ya bar musu matarsa shi kuma ya ƙi yarda.
Asali: Legit.ng