Jami'an Tsaro Sun Yi Nasarar Dakile Mummunan Harin Boko Haram a Kano, Sun Yi Bayani
- Ana cikin tsoro a jihar Kano bayan jami'an tsaro sun dakile wani harin Boko Haram a jihar Kano
- Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasarar dakile harin ne a karamar hukumar Gezawa da ke jihar
- Daraktan yada labarai na rundunar, Onyema Nwachukwu shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 3 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasar dakile harin Boko Haram a jihar Kano.
Wannan na cikin wata sanarwa ce da daraktan yada labarai na rundunar, Onyema Nwachukwu ya fitar a yau Juma'a 3 ga watan Nuwamba.
Sanarwar da jami'an sojin su ka fitar kan harin Kano?
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta ce an kai samamen ne a safiyar yau Juma'a 3 ga watan Nuwamba inda ta kwace muggan makamai a hunnun 'yan ta'addan.
Wane martani sojin kasar su ka yi a harin Kano?
Onyema ya ce rundunar ta yi nasarar dakile harin ne a karamar hukumar Gezawa da ke cikin jihar, cewar Punch.
Ya ce yayin samamen, sun yi nasarar cafke wasu da ke zargi mutum biyu tare da kwato muggan makamai a hannunsu, cewar The Nation.
Sanarwar ta ce:
"Jami'an hadin gwiwa ta sojoji da hukumar DSS sun yi nasarar dakile harin Boko Haram a Kano.
"A wata samame da rundunarmu ta kai da jami'an DSS, mun yi nasarar dakile harin a karamar hukumar Gezawa da ke jihar.
"Har ila yau, rundunar ta yi cafke wasu mutum biyu da ake zargi inda aka kwato muggan makamai a hannunsu."
Wannan na zuwa ne yayin da jami'an sojin ke samun nasara kan 'yan ta'addan a Arewa maso Gabas.
'Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kano
A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari wasu yankunan karkara a jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a kauyen Yola da ke karamar hukumar Karaye da ke jihar inda aka hallaka mutane da dama.
Arewa maso Yamma na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara.
Asali: Legit.ng