Gwamnatin Kano Ta Yi wa Ma’aikata 231 Karin Girma a Wasu Hukumomi
- Gwamna Abba Kabir ya amince da karin girma ga wasu ma'aikata har guda 231 a ma'aikatu daban-daban da ke fadin jihar
- Hukumar kula da ma'akata ta jihar ita ta amince da karin girman inda ta shawarci wadanda abin ya shafa su saka wa gwamnati
- Daraktan yada labarai a ma'aikatar, Musa Garba shi a bayyana haka a yau Juma'a 3 ga watan Nuwamba a jihar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kara wa ma'aikata 231 girma a wasu ma'aikatu da hukumomin jihar.
Hukumar ma'aikata ta jihar ta amince da karin girman wanda mafi yawa yafi shafar manyan ma'aikatan jihar, cewar Punch.
Yaushe ma'aikatan su ka samu karin girma a Kano?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai, Musa Garba ya fitar a yau Juma'a 3 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garba ya ce shugaban ma'aikatar, Umar Minjibir shi ya tabbatar da haka yayin wata ganawa a ma'aikatar, cewar NewsNow.
Munjibir daga bisani ya bukaci wadanda su ka samu wannan damar da su saka wa gwamnati wurin yin aiki tukuru.
Wane shawara aka bai wa ma'aikatan a Kano?
Ya kuma bukace su da su zamo ma su gudanar da aikin su don samun sakamako mai kyau.
Ya ce:
"Ina son yin amfani da wannan daman don rokon wadanda su ka samu karin girman da su saka wa gwamnati wurin yin aiki da gaskiya a ma'aikatunsu."
Ya kuma bukace su da su bi dukkan dokokin ma'aikatunsu don samun biyan bukata kamar yadda kundin tsari ya tanadar, SolaceBase ta tattaro.
Abba Kabir ya ware kudade don 'yan fansho
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ce gwamnatinsu ta ware fiye da biliyan shida don biyan 'yan fansho hakkokinsu.
Abba ya ce daga cikin wadanda za a biya hakkokin akwai wadanda su ka rasa ransu yayin da su ke aiki a jihar.
Gwamnan ya soki tsohuwar gwamnatin Ganduje da wulakanta ma'aikan jihar ba tare da kula wa da su ba.
Asali: Legit.ng