An Kusa Fara Samun Fetur a Legas, NNPC Zai Warewa Dangote Danyen Mai a Disamba

An Kusa Fara Samun Fetur a Legas, NNPC Zai Warewa Dangote Danyen Mai a Disamba

  • Watakila gwamnatin tarayya ta karkashin NNPCL za ta shiga yarjejeniya da matatar man da Aliko Dangote ya gina a Legas
  • Zuwa Diamba Kamfanin NNPCL zai fara ba Dangote litoci miliyan shida na danyen man da aka hako a Najeriya domin a tace
  • Idan matatar da sauran kananan matatu su ka samu mai a gida, za a samu saukin man fetur, dizil, kananziri zuwa man jirgi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kamfanin mai na kasa wanda aka fi sani da NNPCL kamar yadda ake sa rai, zai warewa matatar Dangote danyen mai a Disamba.

The Cable ta fitar da labari cewa matatar Dangote za ta samu lita miliyan shida na danyen mai da za a tace ta hannun kamfanin NNPCL.

Kara karanta wannan

A bar batun man fetur; Tinubu ya fadi inda Najeriya za ta koma samun kudin shiga

Dangote
Matatar Dangote a Lekki Hoto: www.hydrocarbons-technology.com
Asali: UGC

Wannan yunkuri zai taimaka wajen taimaki kamfanonin gida wanda zai inganta tattalin arziki duk da ana neman komawa ma'adanai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarjejeniyar NNPCL da matatar Dangote

Wata majiya ta ce an ci ma wannan matsaya ne yayin da ake shirin kammala yarjejeniyar ciniki na SPA tskanin kamfanin man da matatar.

Ana sa ran da ‘yan kwanaki kadan a karasa yarjejeniyar, kowane bangare ya sa hannu bayan an dade ana jiran matatun gida su fara aiki.

Wasu da su kan san abubuwan da ke faruwa a cikin gida, sun shaidawa jaridar NNPCL zai rika saidawa Dangote danyen mai a farashin kasuwa.

Kamfanin ba zai tsawwala farashi ba, haka zalika Dangote ba zai samu man a araha banza ba. Burin shi ne fetur ya wadata a farashi mai kyau.

Dokar PIA za ta taimakawa Dangote

Sashe na 109 na dokar PIA ta shekarar 2021 ta wajabtawa NNPCL bada danyen mai ga matatunta na gida da ke Fatakwal, Warri da garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Kafin a je ko ina, baya ga matatun da ke hannun gwamnati, wajibin kamfanin ne ya ba irinsu matatar Dangote danyen man da za su iya tacewa.

Rahoton ya nuna dokar ta ce za a rika saida gangunan danyen man da aka hako a Najeriya ga ‘yan kasuwan gida ne a lokacin da aka bukata.

Ba a ba matatar Dangote danyen mai

Wani abin kunya da aka ji labari shi ne a halin yanzu gwamnati ta gagara bada danyen mai ga matatun gida domin fara fitowa da fetur da dizil.

Alamu sun nuna gwamnati ba ta hako mai sosai a Neja-Delta kuma an shiga yarjejeniya da kamfanonin waje da ke karbe duk abin da aka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng